✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanke lantarki: Al’ummar Nijar na shirin maka Najeriya a kotu

Al'ummar Nijar na shirin maka gwamantin Najeriya a kotu kan yanke wa kasarsu wutar lantarki

Al’ummar Jamhuriyar Nijar na shirin maka gwamantin Najeriya a kotu saboda yanke wa kasarsu wutar lantarki da ya jefa su cikin kunci

Miliyon al’ummar kasar sun shiga halin ha’ula’i tun bayan da Najeriya ta yanke wa kasarsu wutar lantarki, kuma har yanzu ba ta dawo da shi ba.

Mazauna da jami’an jakadanci a kasar sun shaida wa wakilanmu cewa yanke wutar ya jefa asibitoci cikin halin ha’ula’i, saboda rashin yadda za su adana alluran riga-kafi da sauran magunguna.

A tsakanin al’umma kuma, ’yan daidaikun mutane da ke da wadatar sayen janareto da kudin sa mai ne ke lallabwa su samu wuta.

Za mu maka Najeriya a kotu —CODDAE

Kungiyar kare hakkin samun makamashi a Nijar (CODDAE) da ke aikin bunkasa tattalin arziki, kirkire-kirkire, fasaha da cigaba a Nijar, ta yi alkawarin maka Najeriya a kotu kan yanke wa kasar wuta.

Shugaban CODDAE, Malam Moustafa Khadi, ya ce yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla ba ta da wata alaka da ECOWAS, don haka tana gaba da ra’ayin ECOWAS.

“Yanke wutar ya jefa rayuwarmu cikin matsi, babu ruwan sha, babu lantari, harkokin kasuwanci sun tsaya.

“Muna kammala shirye-shiryen maka gwamnatin Najeriya a kotu domin ta biya diyyar wadannan asara  da ta ja wa al’ummar Nijar,” in ji shi.

Babu wuta a manyan biranen Nijar

A halin yanzu dai, babu wutar lantarki na gwamnati a biranan Yamai, Maradi da Zindar, sauran sassan kasar da ke samu kuma sukan dade babu ita.

Tun ranar 2 ga watan Agusta Najeriya ta yanke wutar lantarki mai karfin megawatt 150 da take ba wa Nijar a wani bangare na takunkumin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka  (ECOWAS) da nufin dawo da mulkin dimokuradiyya a kasar, bayan sojoji sun hambarar da gwamantin Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Kamfanin wutar lantarkin Nijar, Nigeelec ya ce daga cikin matakin da ECOWAS ta dauka na sanya wa Nijar takunkumi, har da na katse abubuwan more rayuwa.

Nijar ta fi dogaro da Najeriya wajen samun wutar lantarki, inda a kullum Najeriya ke ba ta wuta mai karfin megawatt 150.

Daukewar wutar lantarki a Nijar bakon abu ne, amma yanzu abin ya fara zama jiki, tun bayan da Najeriya ta yanke mata wuta a bisa bukatar ECOWAS.

‘Muna cikin kunci’

Wata malamar jinya a Nijar, Halimatou Mani, da ke yankin Tsibiri mai nisa kilomita 14 daga birnin Maradi ta ce yanke wutar da Najeriya ta yi ya jefa su a cikin kunci.

“A nan ba mu saba da dauke wutar lantarki ba, uwa uba kuma mutane ’yan kalilan ke da janareto.

“Abin da Najeriya ta yi ya jefa iyalai cikin kunci, babu yadda za a adana kaya masu saurin lalacewa,” in ji Halimatou.

Wani dan tireda a Maradi, Ibrahima, ya roki gwamnatin Najeriya ta maido da wutar da ta yanke wa Nijar.

“Rayuwa al’umma ya kamata a ba wa muhimmanci kafin siyasa. Mata na kananan yara sai mutuwa suke a asibitoci, musamman a kauyuka, inda babu wata hanyar samun wutar lantarki sai ta gwamnati.

“Su ma masu juyin mulki ina rokon su da su sauko su tattauna da ECOWAS saboda al’ummar kasar nan da suke son su mulka.

“Ita ma ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu na Najeriya, ina rokon ta, don Allah ta yi tunanin wasu hanyoyin dawo da Bazoum, ta bar azabtar da mu,” in ji Ibrahim.

Ya bayyana cewa harkokin kasuwancinsu sun durukushe, “rufe boda kadai ya jefa jama’a cikin kangi, mutane sun rasa hanyoyin samunsu. Ina fata ita babbar kungiyar Afirka, AU za ta samo wata hanyar ta daban domin magance matsalar.”

A ranar 19 a Agusta, wakilin Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Nijar, Stefano Savi, ya yi gargadin cewa rikicin kasar zai jefa miliyoyin yara cikin matsalar yunwa.

“Rikicin na barazana ga miliyoyin yara da ke matukar bukatar agaji, kuma tun kafin tasowar rikicin yara miliyan 1.5 ne aka yi hasashen za su yi fama da cutar tamowa a kasar a bana, sakamakon matsin rayuwa da tsadar kayan masarufi.

‘Ya kamata Najeriya ta guji irin rikicin Kogin Nilu’ —Lolo

Tsohon Jakadan Najeriya a Habasha, Bulus Zom Lolo ya ce yanke wutar da Najeriya ta yi zai iya jawo mata babbar matsala a nan gaba.

Ya ce bayyana cewa hakan tamkar fargar da Nijar ce, ta mayar da hankali wajen samar wa kanta wutar, wanda kuma zai iya jawo wa na Najeriya matsala.

Ya ce duk da cwea Najeriya ta yi biyayya ne ga umarnin ECOWAS, “amma ba na tunanin ECOWAS ta ayyana takamaiman matakin da take so Najeriya ta dauka, don haka da sai kasar ta dubi wani banngare ba na lantarki ba.

Tsohon jakadan ya ce duk da cewa gwamnati ce za ta iya bayyana dalilin daukar matakin, “amma a zahiri tamkar ta farkar da Nijar ne. Wata rana za su iya wayan gari su ce za su fara samar da lantarkinsu a cikin gida.

“Kuma idan suka gina dam din da za su yi amfani da shi, to zai hana gangarowar ruwa zuwa Kogin Nija da kuma dam din Kainji da na Shiroro da ke Najeriya,” wadanda su ne tushen wutar lantarkin Najeriya.

Hakan shi ne kwatankwacin abin da ya faru a Gabashin Afirka, tsakanin Habasha da Masar da kuma Sudan, inda Habasha da ke kusa da ruwan Kogin Nilu, ta yanke shawarar gina madatsar ruwanta domin samar da wutar lantarki.

Wannan ya sa Sudan da Masar , da ke gangare, wadda a baya ita ke ba wa Habasa wutar lantarki, ta ke gani tamkar barazana ga rayuwarta.

“Sudan da Masar sun fio kai da fata suna yakar ’yancin Habasha na amfani da ruwa domin ci gabana, saboda kawai ruwan da ya taso daga kasarta ya ratsa ta cikin kasarsu.

“Wannan shi ne kwatankwacin abin da ake ciki tsakanin Najeriya da Nijar, abu ne da ke bukatar  tattaunawa da fahimta

“Idan Nijar wadda da kasarta ruwan ya taso tna a burin gina dan dinta domin samar da wutar lantarki a cikin gida, to yanzu Najeriya ta daba wa kannta wuka, ta ba su hujjar yin abin da suke da buri” in ji shi.

Matsayin yarjejeniyar lantarkin Najeriya da Nijar

Yarjejeniyar kasa da kasa da Najeriya da Nijar suka kulla ta tanadi ba wa Nijar wani kaso na wutar lantarkin da Najeriya ke samarwa daga Madatsar Ruwa ta Kainji.

Tsohon Jakadan Najeriya a Kuwait, Haruna Garba, ya ce kuskure ne yanke wutar Nijar da da Najeriya ta yi, ko da kuwa yaki kasashen suke yi, saboda yarjejeniya suka yi.

“Tun da dimokuradiyyarmu ta fara karfi, ya kamata gwamnati na nemi shawarar kwararru kafin daukar mataki kan abin da ya shafi diflomasiyya.

“Akwai dalilan diflomasiya, shi ya sa duk da cewa muna ba su wutar a matsayin tukwici, amma ba kyauta ba ne, biya suke yi.

“Don haka yanke wutar asarar kudaden shiga ne ga Kamfanin Samar da Wuta na Kasa (TCN), to ta yaya za a cike gibin da aka samu?

“Ko a lokacin yaki babban laifi ne ka hana abokan gaba wutar lantarki da ruwan sha da asibiti da sauran muhimman abubuwan amfani.

“ECOWAS dai ta nemi ta razana masu juyin mulkin ne, su kuma suka yi biris da ita, don haka ba abin kunya ba ne, kungiyar ta janye,” in ji shi.

Wani tsohon ma’aikacin harkokin wajen Najeriya, Ilyasu Gadu, ya ce yanke wutar da nufin matsa wa sojojin su dawo da Bazoum kan mulkinsa na da tasiri mai yawa.

“Nijar na shirin gina dam a kan kogin Neja, wanda idan ta yi, zai rage yawan ruwan da ke zuwa Kainji,” in ji Iliyasu Gadu.

Ya ce tun da farko ya kamata Shugaba Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dokoki wajen duk matakin da zai dauka kan yarjejeniya a irin wadannan yanayi.

Ya shawarci gwamnati ta rika bin ka’ida a duk abin da za ta yi, saboda nan gaba, saboda, “da wannan abin da Najeriya ta yi gaban kanta ta yi wa Nijar, nan gaba babu kasar da za ta aminta da ita wajen kulla yarjejeniya.

“Wasu al’ummar na ganin Najeriya ba wadda za a yarda da ita ba ce, don haka sun fara neman wasu abokan kulla kawance, wanda hakan zai shafi kasar nan, domin akwai wadanda ke shirye su kulla kawance da su.”

Gadu ya ce Najeriya ba ta yi abin da ya dace ba, kuma abin da ya faru zai yi mummunan tasiri

“Tabbas ba ma son mulkin soji, muna so a dawo da dimokuradiyya, amma abin da kasarmu ta yi kuma baya-ba-zani ne, domin idan Nijar ta ce za ta rama, to tabbas za mu samu matsala,” in ji shi.

Nijar na gina tasar samar da 130mw na lantarki 

Aminiya ta gano a halin yanzu Nijar na gina tashar samar da wutar lantarki na cikin gida mai karfin megawatt 130 a yankin Tillabéri mai nisan kilomita 180 daga birnin Yamai.

Sakatare-Janar na Jam’iyyar PNDS Tarayya, Alhaji Boubacar Sabo, ya ce kasar ta yi nisa da gida dam din Kandadji a kan Kogin Neja, wanda take fatan kammalawa nan da  shekara biyu.

Ya ce kasar ta togara da Najeriya wajen samun kashe 70 na wutar lantarkinta, amma duk da haka za ta iya lallabawa ba da wutar Najeriya ba, har zuwa lokacin da za ta kammala nata dam din.

Binciken Aminiya ya gano cewa dam din Kandadji na Nijar zai haddasa karancin ruwa a dam din Kainji da ke Najeriya, wanda a halin yanzu shi ne ya jefa Nijar cikin duhu.

Yunkurinmu na tattauanwa da shugaban kamfanin TCN, Sule Abdulaziz, ya ci tura, amma wata  kwkkwarar majiya a kamfanin ta shaida mana ceaw “Megawatt 150, ake wa ba Nijar, amma wani lokaci yakan dan yi kasa, ko ya yi sama”.

Gwamnatocin Nijar karkashin Bazoum da magabacinsa, Mahamadou Issoufou sun yi aiki wurjanjam domin ganin kammaluwar tashar lantarki ta Kandadji domin kasar ta dogara da kanta.

Ba da jimawa ba kafin hambarar da Bazoum ya kai ziyarar gani da ido a tashar lantarkin, inda a lokacin ya ce, “an magance duk wasu matsalo da batun biyan kudi. Nan da watanni masu zuwa aikin zai tafi yadda ake so.”

Ba yau farau ba

Ko da yake bincike ya gano cewa an sha dage lokacin kammala aikin tashar wutar lantarki ta Nijar.

Da farko kamfanin Zaroubegevodstroï (ZVS) na kasar Rasha aka fara ba wa aikin, kafin yanzu a ba wa kamfanin Gezhouba Group Company Limited (CGGC) na kasar China.

Hukumomin kasashen duniya irin su Bankin Duniya, Bankin Raya Afirka,  Hukumar Bunkasa Cigaban Faransan, Bankin Musulunci da suransu ne ke da hannu wajen gina dan din.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Dalhatu Liman (Abuja) & Hamisu Kabir Matazu (Maiduguri).