Wata mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da ‘Ida’ wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan saman da aka tafka a Arewa maso Gabashin Amurka ta hallaka akalla mutum 36 kamar yadda hukumomi suka tabbatar ranar Alhamis.
Gwamnan Jihar New Jersy da ke Amurkan, Phil Murphy ya tabbatar da cewa akalla mutum 23 ne ’yan asalin Jihar suka rasu sakamakon guguwar, yayin da Magajin Garin birnin New York kuma Bill de Blasio ya ce ta kashe mutum 13 a Jiharsa.
- Lauya na neman gwamnati ta biya shi diyyar N10m saboda kafa shinge a hanya
- Umarnin kotu ba zai hana mu gudanar da tarukan ranar Asabar ba – APC
Rahotanni sun kuma ce wasu mutanen sun mutu a makwabtan Jihohin Pennsylvania da Maryland.
Burbushin guguwar dai ya jawo gagarumar asara a daukacin Gabashin Amurka yayin da aka fuskanci wata annobar ta ambaliyar ruwa a birnin New York.
Gwamnan Jihar ta New York, Kathy Hochul ya ce tuni ya bukaci Gwamnatin kasar ta ayyana dokar ta-baci a hukumance a gundumomi 14 da annobar ta shafa.
A wurare da dama na birnin dai an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa da yammacin Alhamis bayan ambaliyar ta shafe daukacin hanyoyin wasu sassan birnin.
A birnin New Jersey ma, guguwar ta yaye rufin gidaje da dama da kuma lalata wasu masu yawa, sannan ta tilasta rufe filayen jirgin sama na biranen.
Akalla gidaje 100,000 ne a yankin rahotanni suka ce sun rasa wutar lantarki bayan wani mamakon ruwan sama.
Guguwar ta Ida dai bayanai sun nuna ta fi ta Henri da aka taba yi a baya barna.
Shekarar bana dai ba kawai ta kasance mai dauke da zafi da kuma hasken rana ba ne, ta kuma kasance mafi yawan ruwan sama a tarihin yankin na Amurka. (NAN)