A kasar Amurka, wata mahaukaciyar guguwa da take ci gaba da bazuwa a wasu jihohin kasar ta hallaka sama da mutum 100, ta kuma lalata gine-gine da dama.
Tuni dai Shugaban Kasar, Joe Biden, ya yi alkawarin taimaka wa jihohin da guguwar ta yi wa ta’adi da duk abin da suke bukata.
- Babbar mota ta hallaka yara masu roron wake 14 a Saminaka
- An sace uwa da ’ya’yanta hudu a Kaduna —’Yan sanda
Guguwar dai, wacce masu harsashen yanayi suka ce ba kasafai ake fuskantarta a watannin sanyi ba, ta lalata wata masana’anta a jihohin Mayfield da Kentucky, sannan ta lalata wani gidan rainon yara a Arkansas, ta kuma kashe akalla ma’aikata shida a wani wajen ajiyar kaya a Jihar Illinois.
Shugaba Biden ranar Asabar, ya bayyana guguwar a matsayin daya daga cikin mafiya muni a tarihi, inda ya ayyana bayar da wani taimakon gaggawa ga Jihar Kentucky, wacce ita ce lamarin ya fi shafa ta hanyar kashe mata mutum 22.
Shi ma Gwamnan Jihar ta Kentucky, Andy Beshear, ya ce guguwar ita ce mafi muni a tarihin Jihar.
Ya ce akalla ma’aikata 40 ne aka ceto daga ma’aikatar wacce take da sama da ma’aikata 110 a cikinta lokacin da aka fara guguwar ta yi kaca-kaca.
Gwamnan ya ce ba karamar sa’a za a ci ba a samu ceto wani mutum mai rai daga cikin baraguzan ginin, inda ya ce akwai yiwuwar a samu sama da mutum 100 da suka rasu a jihar kawai.
Wasu hotuna da bidiyo dai da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda guguwar ta ruguje gine-gine da dama a jihar Mayfield, yayin da motocin da aka ajiye a waje kuma suka kusa nitsewa a baraguzai.
A yankin Edwardsville na Jihar Illinois, Shugaban Hukumar Kashe Gobara, James Whiteford ya ce akalla mutum shida ne suka mutu lokacin da wajen ajiyar kayan ya rushe, wasu 45 kuma suka tsallaki rijiya da baya.