✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe masu hakar ma’adinai 8 a Filato

Mahara sun kashe mutum takwas a wurin hakar ma’adinai a Kuru, Jihar Filato.

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kashe mutum takwas a wurin hakar ma’adinai a yankin Kuru na Jihar Filato.

Gwamna Simon Lalong, ya bayyana takaicinsa kan sabon harin na ranar Juma’a, sannan ya umarci jami’an tsaro su kamo maharan domin su fuskanci hukunci.

Lalong ya bayyana harin da cewa yunkuri ne na wasu marasa kishi da ke neman tayar da fitina da sanya tsoro a zukatan al’umma bayan samuwar kwanciyar hankali a Jihar Filato.

Ya kuma jajanta wa iyalan mamatan tare da jaddada cewa ba uzuri ba ne ga jami’an tsaro su ce ba a san maharan ba, don haka nan gaba ba zai lamunta ba.

Gwamnan ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ba wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar taimaka musu da bayanai ta hannun sarakuna da ’yan sa-kai da ’yan banga domin dakile ayyukan miyagun iri.