✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da uwa da ’ya’yanta hudu a Kaduna

Iyalan wani tela ne aka yi garkuwa da su a unguwar Barakallahu mai iyaka da barikin soji

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da ’ya’yanta hudu a unguwar Barakallahu mai iyaka da barikin sojin sama a birnin Kaduna a ranar Juma’a.

Mahaifin yaran kuma mijin matar Abdulsalam Haruna wanda tela ne ya ce da misalin karfe 1.30 na safiyar Juma’a ne ake dauke matar tasa da ’ya’ya hudu.

“Sun tafi da hudu daga cikin ’ya’yana da kuma mahaifiyarsu. Biyu daga cikin yaran daliban jami’a ne daya na makarantar sakandare daya kuma na aji shida a firamare”, kamar yadda ya shaida wa wakiliyarmu.

Ya ce “har yanzu ina mamakin abin da ya sa suka kawo min hari, ni fa tela ne ba mai kudi ba.

“Shekara biyu ke nan da na dawo nan da zama daga Unguwar Shanu, amma kuma ga irin abin da ya faru”.

Wani mazaunin yankin, Alhaji Jamilu, ya shaida wa wakilanmu cewa maharan sun kai farmakin ne da tsakar dare inda suka yi awon gaba da iyalan ‘yan gida daya.

“Karar harbi ta tashe mu daga barci, mun dauka daga barikin sojin sama ne da ke bayanmu, amma sai muka fahimci akwai matsala saboda karar da muka ji a layin da ke bayanmu.

“Da na je masallaci sallar asuba, da misalin karfe 6.00 sai ake shaida min cewa masu garkuwa da mutane ne suka yi ta bi gida-gida, kuma sun yi awon gaba da yara kanana guda hudu.