Mahara sun farmaki wasu unguwanni biyu a yankin Dutsen Abba da ke Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, inda suka sace mutum 10.
Rahotanni sun ce maharan sun kuma kashe mutum daya a harin da suka kai a daren Juma’a.
- Duk da tubar dubban ’yan ta’adda a dage da addu’o’i —Zulum
- Yadda ake hada ‘juice’ din kankana da abarba
Wata majiya ta bayyana yadda ’yan bindigar suka farmaki kauyen Gabari da misalin karfe 11:00 na daren Juma’a, sannan suka sace wasu mutum biyu.
Kazalika, sun farmaki kauyen Kafin Mardanni, wanda a nan ma suka shiga gida-gida suka sace mutum takwas.
Majiyar ta shaida cewar, maharan sun yi dauki ba dadi da jami’an tsaro wanda hakan ya sanya su tserewa daga maboyarsu.
Wani shaidar gani da ido, ya bayyana mana cewar maharan sun harbe wani mutum a kan hanyar kauyen Kufena yayin da suka yi kacibus da shi.
“Sun dauka yana daga cikin mutanen da suka biyo su, saboda sun gan shi akan babur, nan take suka harbe shi da bindiga,” a cewar majiyar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mahaifin wani karamin yaro da suka sace mai suna Mallam Ibrahim Mai Shago Gabari, ya ce an yi nasarar ceto ’yarsa da aka sanya ranar aurenta jim kadan bayan sace da maharan suka yi.
“A kan idona suka tafi da ita lokacin da suka shigo cikin gidana, sun ce kowa ya kwanta a kasa sannan suka dinga harbi a iska.
“Bayan ta fito daga dakinta suka tambaye ta sunanta, ta ce musu sunanta Fatima, nan take suka ce ita dama suke nema don haka suka yi awon gaba da ita.
“Sun shiga gidan makocina nan ma suka tafi da ’yarsa amma ba su taba kowa ba.
“Bayan kamar awa uku sai ga wasu ’yan banga sun dawo mana da ’ya’yanmu bayan gumurzu da suka tafka da maharan,” kamar yadda ya bayyana.