✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kona sakatariyar karamar hukuma a Kogi

Hukuma ta ce harin bai shafi ofishin INEC ba

Wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari tare da kona Sakatariyar Karamar Hukumar Okehi da ke yankin Obagende a Jihar Kogi.

Ana zargin harin ya shafi bangaren ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke sakatariyar.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP William Aya, ya ce, “Wani bangare na sakatariyar wutar ta lalata wanda hakan bai shafi INEC ba kamar yadda aka yada a kafofin sada zumunta na zamani.”

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Enesi ya ce da alama maharan sun dana abu mai fashewa wanda a sakamakon haka wani sahen ginin sakatariyar ya kone.

Ya ce, “Mun yi sa’a wauta ba ta shafi bangaren INEC ba wanda ke dab da sashen da ya kone.

“Ba domin haka ba, da kayayyaki da dama sun kone, fashewar ta lalata komai na sashen da ya ci wuta,” in ji Enesi.

Mai bai wa gwamnatin jihar shawara kan harkar tsaro, Jerry Omodara, ya tabbatar da aukuwar harin a ranar Talata.

Ya ce aikin mahassada ne wadanda ba sa son ganin zabe mai zuwa ya yi nasara.

SP Aya ya ce babu wanda ya mutu sakamakon harin, kuma Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Hakeem Adesina Yusuf, ya tura kwararrun masu bincike domin tantance abin da ya fashe din.

Ya bukaci jama’ar yankin kowa ya ci gaba da harkokinsa ba tare da wani tsoro ko fargaba ba.