✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa

Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun harbe mutum tara har lahira tare da jikkata wasu da dama a Ƙaramar Hukumar Karu ta…

Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun harbe mutum tara har lahira tare da jikkata wasu da dama a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Da misalin ƙarfe 8 na dare ne maharan suka kai farmaki suna harbi kan mai uwa da wabi a yankin Tattara ranar Asabar.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “bagatatan suka far mana a cikin dare, mutum tara sun rasu wasu biyu na kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai baya ga wasu da suka raunuka da dama.”

Kimanin shekara guda ke nan da aka kai makamancin harin tare da ƙona gidaje a yankin na Tattara.

Wakilinmu ya lura ’yan sanda na ƙoƙarin daidaita al’amura a yankin a ranar Lahadi, sai dai ƙoƙarinsa na yin magana da kakakin rundunar na jihar Nasarawa bai yi nasara ba, kuma wayar jami’in ba ta shiga.