✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 4, sun jikkata wasu 5 a Zariya

An kai harin ne Anguwar Dankali da ke Zariya

Wasu gungun mahara sun kai hari Anguwar Dankali da ke Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum 4 tare da jikkata wasu 5.

Har ila yau, maharan sun kuma yi awon gaba da mata 3 da jariri a goye, bayan artabun da suka yi da jami’an tsaro wadanda daga baya suka sako matan, in ji mazauna anguwar.

Harin ya faru ne a daren Juma’a da misalin karfe 10.30 na dare.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, Sarkin anguwar Dankali, Mallam Sunusi Yusuf ya ce “Maharan sun yi ta harbe-harben kan mai uwa da wabi lokacin da suka shiga anguwar, inda daga bisani suka harbe mutum 9 kuma nan take mutane 4 suka rasa ran su, biyar kuma suka sami munanan raunuka.

Sarkin ya kara da cewa, sakamakon tallafin da jami’an tsaro na yankin suka kai, maharan sun arce daji da wasu mata 3 da jariri da suka dauka a anguwar.

Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da Dahiru Tsalha Wawo, Bashir Salisu, Umar Yahuza da kuma Umar Bako.

Wadanda kuma suka sami munanan raunuka kuma suke kwance a gadon asibiti a halin yanzu sun hada da Abubakar Yahuza, Bala Shamaki, Aliyu Ahmed, da kuma Abdullahi Mamuda.

Aminiya ta sami tabbacin kwato sauran mata 3 da jariri da maharan suka yi garkuwa da su a wajen garin Jaji da ke Karamar Hukumar Igabi, sa’ilin da kungiyar ’yan sintiri suka tare su kuma suka sami nasarar kubutar da wadanda suka dauke.

Tuni aka gudanar da jana’izar mamatan hudu tare da binne su a makabartar Bakiin dogo dake anguwar Dankali da safiyar Asabar.

Shi ma da yake nuna alhininsa akan al’amarin, Mai Anguwar da lamarin ya faru, Alhaji Musa Tanko, ya ce al’umomin yankin na cikin fargaba da tashin hankali bisa wannan iftila’in da ya faru.

Ya kara nuna fargabarsa bisa yankin ya zama wajen kai hare-haren ’yan ta’adda a dan tsakanin nan.

Mai anguwar ya yi nuni da cewa, “Duk da dai wannan shi ne karo na farko da maharan suka farmaki anguwar, amma kuma ayyukan maharan na faruwa a makwabtansu da ke Wusasa da Kuregu a kusan kowanne mako, wanda duk al’umma daya ce.

Sai yayi kira da a yawaita addu’o’i tare da yin kira ga jami’an tsaro da su tsaurara tsaro a yankin.

Da wakilin mu ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar a Jihar, ASP Mansir Hassan, ya ce a ba shi lokaci ya bincika labarin sannan ya sanar da abin da ya faru.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai kira ba.