✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Isra’ila da Hamas: An kashe Falasdinawa 198, Yahudawa 40

Rikicin na zuwa ne bayan Hamas ta kaddamar da hari kan Isra'ila

Ya zuwa yanzu, akalla Falasdinawa 198 ne suka mutu sakamakon harin ramuwar gayya da Isra’ila ta kaddamar a kan Zirin Gaza, kamar yadda hukumomin lafiya suka tabbatar.

Sun kuma ce akalla wasu mutum 1,610 ne yanzu haka suka ji raunuka.

Isra’ila dai ta kaddamar da hare-haren da ta kira na “Takobin Karfe” domin mayar da martani ga harin kungiyar Hamas ta Falasdinawa wadanda suka jefa mata rokoki da safiyar Asabar.

Tun da farko dai Ministan Lafiya da ke Gaza ya ayyana dokar ta-baci a ilahirin fadin yankin.

Isra’ila dai ta kaddamar da hare-hare ta sama har guda 20 a Gaza domin martani ga matakin na kungiyar Hamas a kan ta.

A wani labarin kuma, kafafen yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa akalla Yahudawa 40 ne aka kashe ya zuwa yanzu, wasu 740 kuma suka jikkata.

Kafar yada labarai ta N12 ce dai ta rawaito haka, kodayake har yanzu babu tabbaci kan hakan daga hukumomi.

Sai dai alkaluman da hukumomin Isra’ila suka fitar sun tabbatar da kashe Yahudawa 22, sai kuma wasu 545 da suka jikkata.