✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya ƙazanta tsakanin Isra’ilawa da Falisɗinawa a Zirin Gaza

Yanzu haka dai dakarun na Isra’ila sun fara mayar da martani.

Kungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta kaddamar da wani harin mafi girma a tsawon shekaru ga Isra’ila a ranar Asabar.

A yau Asabar 7 ga watan Octoba, kungiyar mai gwagwarmaya da makamai ta Falasɗinawa ta harba wasu wasu gwamman rokoki da daga yankin Zirin Gaza zuwa cikin yankin da kasar Isra’ila ta kwace, al’amarin da ya kawo karshen tsagaita wutar da aka cimma tun bayan barkewar yakin kwanaki 5 da aka gwabza a cikin watan mayun da ya gabata.

Ma’aikatar lafiya ta Isra’ila ta bayyana cewa akalla mutum 545 aka raunata a harin da Falasɗinawan suka kai.

Haka kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra’ila ta ce akalla ’yan Isra’ila 22 aka kashe sakamakon harin.

Rahotanni sun ce mayakan na Hamas sun shammaci dakarun na Isra’ila da safiyar Asabar inda suka kutsa cikin Isra’ila ta ruwa da ta kan tudu tare da bude wuta.

Haka kuma mayakan na Hamas sun kai farmaki wasu sansanonin soji na Isra’ila.

Gidan rediyon Isra’ila ya bayyana cewa mayakan Hamas sun yi garkuwa da dakarun Isra’ila 35.

Wani mai magana da yawun sojojin Isra’ila ya bayyana cewa Falasdinawa sun harba makaman roka akalla 2,500 cikin Isra’ila, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.

Shugaban sojin Hamas, Mohammed Deif ya sanar da cewa sun soma wani shiri mai suna “Operation Al-Aqsa Storm.”

“A yau mutane suna sake samun juyin-juya halinsu,” kamar yadda ya bayyana a wani sakon murya a lokacin da ya yi kira ga Falasdinawa daga gabashin Birnin Kudus zuwa Arewacin Isra’ila kan su shiga yaki domin yakar “wadanda suka mamaye su da kuma rusa bango.”

Wannan harin na zuwa ne bayan an kashe wani Bafalasdine a lokacin wata arangama tsakanin wasu mazauna Isra’ila ba bisa ka’ida ba a birnin Huwara da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye inda har aka yi sabon rikici a lokacin jana’izarsa har mutum tara suka jikkata.

An harba makaman roka

An harba makaman roka daga wasu sassa na yankunan da Falasdinawa suke tun daga 06:30 na safe, inda aka ci gaba da harba makaman har tsawon minti talatin, kamar yadda wani dan jarida na Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya bayyana.

A cikin wata nadaddiyar murya da aka yada ta kafar TV din Al-Aqsa, ta kungiyar Hamas, komadan mayakan Ezzedine al-Qassam Mohammad Deif, ya bayyaa cewa, sun kaddamar da hare hare ne, domin kawo karshen mamayen da Isra’ila ke yi wa kasarsu.

Ya kara da cewa, akalla sun harba rokoki sama da dubu 5000 tun da dugun dugun safiyar yau Asabar, kawo lokacin rubuta rahoton.

Ya kuma bukaci duk wani bafalastinen da ke da makami ajiye a gidansa da cewa, lokaci ya yi da ya kamata ya fito da shi ya yi aiki da shi.

Sojojin Isra’ila sun kunna jiniya ta gargadi a fadin kudancin kasar, inda ’yan sanda suka gargadi jama’a da su tsaya kusa da wuraren da ake bayar da kariya daga hare-haren bama-bamai.

An ta jin karar hare-hare a kusa da birnin Tel Aviv da kuma wajen Birnin Kudus da aka mamaye.

Isra’ila ta zagaye tare da hana shige da fice ba da izini ba cikin Gaza tun daga shekarar 2007.

Tun daga lokacin mayakan Falasdinu da kuma sojojin Isra’ila suke fafata yaki.

Takunkumin da aka saka wa Gaza, ya hana mutane da kayayyaki shiga da fita wanda hakan ya jawo koma baya ga tattalin arzikinsu.

Yanzu haka dai dakarun na Isra’ila sun fara mayar da martani abin da ake ganin zai maimaita abin da ya saba faruwa a yankin na malalar jinin babu kakkautawa.

Kasashen Duniya sun soma mayar da martani

Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi ya bayyana cewa kasarsa ta tare da da kuma jaddada goyon baya ga Isra’ila bayan hare-haren da mayakan Gaza suka kaddamar a safiyar yau.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Modi ya ce, “Na yi matukar kaɗuwa da labarin hare-haren ta’addanci a Isra’ila. Muna tare da Isra’ila a wannan mawuyacin halin.”

“We invite all parties to act reasonably and to stay away from impulsive steps that raise tensions,” Erdogan, who strongly supports the Palestinian cause, said following attacks on Israel by Palestinian militants from the Gaza Strip.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci a gaggauta samun jituwa tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa “da su yi aiki mai ma’ana tare da guje wa wani tashin hankali.”

“Muna gayyatar dukkan bangarorin da su yi aiki da hankali da kuma nisantar matakai masu tayar da,” in ji Erdogan.

Muna kara jaddada cewa muna matukar goyon bayan al’ummar Falasɗinu, bayan hare-haren da ’yan gwagwarmayar Falasɗinawan suka kai wa Isra’ila daga Zirin Gaza.

Ministar Harkokin Jamus, Annalena Baerbock ta ce Hamas na ba da gudummawa wajen “karfafa tashe-tashen hankula”, ta kara da cewa Isra’ila “tana da cikakken goyon bayanmu” da “yancin kare kanta daga ta’addanci.”

Yanzu haka mun tuntubi kowane bangare na Isra’ilawa da Falasdinawa da Larabawa,” a cewar Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha, Mikhail Bogdanov.

Bogdanov ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Rasha mai zaman kansa na Interfax, ya kara da cewa: “Hakika, a ko da yaushe muna kira da su guji tashin hankali.”