✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Alassane Ouattara ya rusa gwamnatin Ivory Coast

Za su ci gaba da zama a muƙamansu na ɗan lokaci har sai an naɗa sabon firaminista da ƴan majalisar gwamnati.

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya tube firaministan kasar, Patrick Achi da kuma ministocinsa daga mukamansu.

Ba a faɗi dalilin ɗaukar matakin ba a ranar Juma’a, sai dai ya ce zai kafa sabuwar gwamnati yayin da ya rage shekaru biyu a gudanar da zaben shugabancin kasar.

Shugaban Ouattara ya rattaba hannu kan kudurin doka da ke tsige firaminista da kuma illahirin ministocinsa, kamar dai yadda wata sanarwa da Sakataren Gwamnati Abdourahman Cisse ta nunar.

A wannan sanarwa dai shugaban kasar ya yaba da kamun ludayin firaminista, Patrick Achi da kuma sauran ministocin da suka yi aiki a karkashinsa tsawon shekarun da suka gabata.

“Shugaban ƙasa yana miƙa godiyarsa ga Firaminista Patrick Achi da dukkan mambobin gwamnatinsa kan jajircewarsu da hidimar da suka yi wa ƙasar a tsawon shekaru,” in ji Cisse.

“Za su ci gaba da zama a muƙamansu na ɗan lokaci har sai an naɗa sabon firaminista da ƴan majalisar gwamnati,” ya ƙara da cewa.

Tun ranar 28 ga watan Satumbar da ya gabata ne aka fara yada jita-jitar cewa shugaba Alassan Ouattara yana da niyyar rusa gwamnatin firaminista Achi, wanda ya dare kan wannan mukami a watan Maris na 2021 bayan mutuwar Hamed Bakayoko, wanda ya mutu saboda harbuwa da cutar kansa, wanda shi ma an nada shi kan matsayin ne bayan mutuwar Adamou Gon Coulibaly a 2020.

A watan Afrilun bara ne Achi ya miƙa takardarsa ta barin aiki da ta mambobin gwamnatinsa bayan da Ouattara ya sanar da shirye-shiryensa na rage yawan ministocin gwamnatin.

Mako guda bayan nan ne aka sake zaɓar firaministan.

A shekarar 2025 ne za a gudanar da zaɓe a Ivory Coast. Ouattara, wanda aka sake zaɓarsa a shekarar 2022, har yanzu bai bayyana ko zai sake tsayawa takarar ta gaba ba.

Yanzu haka dai jam’iyyar RDHP mai mulki a kasar na ci gaba da samun karsashi, domin ko a lokacin da aka gudanar da zaben kananan hukumomi a watan jiya, ta lashe fiye da 60% na kujerun da aka yi takarar da a kai.