✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 12 a Jihar Zamfara

Wadansu ’yan bindiga da ake zargin mahara ne, sun mamaye kauyen Bawar Daji da ke karamar Hukumar Anka a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum…

Wadansu ’yan bindiga da ake zargin mahara ne, sun mamaye kauyen Bawar Daji da ke karamar Hukumar Anka a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum 12 a shekaranjiya Laraba.

Mazauna kauyen sun bayyana cewa maharan sun dara 10, inda suka mamaye kauyen da misalin karfe daya na rana, kuma nan take suka bindige mutum hudu, suka gudu. Daga bisani kuma suka sake dawowa bayan awa daya, suka sake kashe wadansu mutum takwas.

Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Muhammad Shehu ya ce mutum uku ne suka rasu. Ya ce ’yan sanda sun fuskanci maharan, wanda ya sanya dole suka gudu zuwa cikin daji. Wannan harin ya faru ne bayan mako biyu da wadansu mahara suka bindige mutum takwas a kauyen Dogon Daji da ke karamar Hukumar Maru a jihar.

A farkon watan Maris din nan  ne aka kashe fitaccen dan fashi da makamin nan, Buharin Daji, wanda tubabben dan fashi, Dogo Gide ya kashe asakamakon  musayar wuta a tsakaninsu, a wani daji da ke kusa da garin dansadau.

Tunda farko dai mazauna yankin da ke fuskantar manyan mahara a karamar Hukumar Anka sun roki Gwamnatin Tarayya ta ba su kariya daga tu’annatin ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane, sun bayyana cewa akwai wani hatsabibi mai suna Gajere da yake addabar yankin da sace mutane yana garkuwa da su, yana amsar kudin fansa.

A tattaunawarsu da Aminiya, wadansu mazauna kauyukan Duhuwa da Dawan Jiya da Gobirawa da Tungar Daji sun ce mafi yawan hare-haren da ke aukuwa a yankunanu, wannan shugaban mahara mai suna Gajere ne ke aiwatar da su.

“Gajere ya zama annoba, tun bayan da ya shiga gungun mahara masu satar dabbobi da sace mutane don kudin fansa, su ne suke addabar yankunanmu,” inji Ali Mustapha, daya daga cikin mazauna yankin.