Shugaban Kasar Burkina Faso, Roch Kabore, ya sanar cewa akalla mutum 100 ne suka mutu a mummunan harin da aka kai kauyen Soulhan da ke Arewa-maso-Gabashin kasar ranar Asabar.
Kabore ya ba da umarnin yin makoki na kwana uku a fadin kasar kan wadanda suka rasa rayukansu a harin.
- Dakatar da Twitter: Za mu hukunta wadanda suka karya doka — Malami
- ’Yan sanda sun cafke ’yan kungiyar IPOB da makamai
Ya ce, “Tuni jami’an tsaro suka bi sahun wadanda suka kai farmakin”, kamar yadda ya bayyana cikin wani jawabi a Facebook.
Sai dai babu wani cikakken bayanin da ya sa ’yan bindigar suka kai farmakin tare da kashe mutum 100 a kasar.
Wannan shi ne hari mafi muni da ya salwantar da rayukan mutane da dama a kasar, kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran kasar (AIB) ya bayyana, inda ya ce adadin wadanda suka rasun zai iya ninkawa.
Da take yi tir da harin ’yan bindigar, Kungiyar Tarayyar Turai (EU), ta hannun Babban Jakadanta, Joseph Borrell, ta ce tilas ne a yi saurin cafko maharan don hukunta su.
Borrell ya kuma bayyana cewar akalla karin mutum 14 sun rasu, bayan da wasu mahara suka kai farmaki a lardin Oudalan da ke yankin Sahel a kasar.
Mahara da dama na kara addabar yankin Sahel na kasar, inda wasu daga cikinsu ke ikirarin hadin gwiwa da kungiyar Al-Qaeda.
Ayyukan ’yan bindiga na ci gaba da kamari a kasar tun daga shekarar 2015.