✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe mutane suna sallah a masallaci a Nijar

Mahara sun bindige mutum 10 suna tsaka da sallah a cikin masallci

Mahara sun kashe wasu mutum 10 a yayin da suke tsaka da sallar Magriba a cikin masallaci a kasar Jamhuriyar Nijar.

’Yan bindigar sun yi wa kauyen Abankor da ke Jihar Tillaberi dirar mikiya ne a kan babura da yammacin ranar Laraba.

“Maharan sun isa kauyen ne a kan babura ana tsakiyar Sallar Magriba suka bude wa masallata wuta,” a cewar wani ganau.

Jihar Tillaberi, inda kauyen Abankor yake a Jamhuriyar Nijar na makawabtaka da kasashen Mali da kuma Burkina Faso.

Hare-haren ’yan bindiga na ta karuwa a yankin tun farkon wannan shekara, musamman a yankunan iyakar jihar da kasashe makwabata.

Majalisar Dinkin Duniyata yi gargadi a farkon watan Oktoba cewa mutun 600,000 mazauna Tillaberi na fuskantar matsalar karancin abinci.