Ana fargabar an kashe kananan yara da mata da yawa a wani hari da aka kai a kauyen Kubat na Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Gwamnan jihar, Simon Bako Lalong, ya tabbatar cewa maharan sun kai harin ne kafin wayewar garin Talata a yayin da mutanen kauyen ke tsaka da barci.
- Yadda da ya yi dambe da ’yan bindiga ya kwaci mahaifinsa a Kano
- Saudiyya ta zartar wa dan kasarta hukuncin kisa kan ta’addanci
Lalong ya yi Allah-wadai da harin, sannan ya umarci jami’an tsaro da su farauto mahran domin su fuskanci hukunci.
Sanarwar da daraktan yada labaran gwamnan, Makut Simon, ya fitar ta ce Lalong ya umarci hukumomin agaci da na zaman lafiya na jihar su ziyarci kuayen domin gano tantance girmar barnar da aka yi domin samar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.