’Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda tare da yin garkuwa da wani dan kasar China da ke aikin titin jirgin kasar Legaz zuwa Ibadan.
’Yan bindigar sun kai harin ne a kauyen Adeaga/Alaagba da ke kan iyakar jihohin Oyo da Ogun.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 26 a kauyen Zamfara
- ’Yan bindiga sun kashe daliban dalibai sun sace wasu a Kebbi
Maharan, da ake zargin makiyaya ne, sanye da bakaken kaya, sun kutsa kai wurin aikin jirgin kasa a kauyen na Adeaga/Alaagba da ke Karamar Hukumar Odeda, suka kashe dan sandan da ke aiki da ma’aikatan China.
A safiyar Alhamis ne kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an ’yan sanda na bincike tare da bin sahun maharan.
Sai dai ya ce ’yan sanda ba su da tabbacin ko Fulani makiyaya ne suka kai harin.
“Da gaske ne an kai harin ranar Laraba, kuma an yi garkuwa da wani dan kasar China da ke aikin titin jirgin kasa, an kuma kashe wani dan sanda da ke aiki tare da su.
“Mun fara binciken yadda harin ya faru tun ranar Laraba, muna kuma da yakinin cewa za mu cafke wadanda suka kai harin.
“An baza kwararrun jami’an tsaronmu a fadin yankin da aka kai harin, kuma nan da wani lokaci za a samu kyakkyawan sakamako,” a cewarsa.