Wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun hallaka dan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar Mazabar Baraza/Dass, Alhaji Musa Mante.
An kashe shi ne ranar Alhamis a gidansa da ke Dass.
Wata majiya ta ce maharan sun yi wa gidan dan majalisar kawanya ne da tsakar dare inda suka yi ta harbe-harbe har suka kashe shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sanda ta Jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa maharan sun kuma yi garkuwa da matan mamacin su biyu da kuma diyarsa mai kimanin shekara daya a duniya.
DSP Ahmad ya ce matan da aka yi garkuwar da su sune Rashida Musa Mante mai shekaru 40, Rahina Musa Mante mai shekaru 35 sai kuma diyar mai suna Fausar Musa Mante.
Ya ce ya zuwa yanzu ba su kai ga tantance ko su wane ne hakikanin maharan ba, ko da yake suna kyautata zaton ‘yan fashi ne.
Ya ce tuni rundunar ta umarci ofishin shiyyarta da ke Dass da ya baza jami’ansa domin fadada bincike tare da farautar ‘yan bindigar.
Idan dai za a iya tunawa, a ‘yan makonnin da suka gabata ne marigayi Musa Mante ya kamu da cutar COVID-19 kuma yana gida yana murmurewa lokacin da maharan suka hallaka shi.