Wasu mahara sun kutsa wata makarantar mabiya aƙidar Shi’a suka harbe dalibai uku har lahira a Jihar Yobe.
A daren Alhamis ne maharan da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Harma ne, suka kutsa makarantar Fadiyya da ke Karamar Geidam suka yi wannan aika-aika.
Aminiya ta gano cewa ɗaliban suna tsaka da barci a cikin fitacciyar makarantar da ke unguwar Hausari ne maharan suka far musu.
Wani ganau ya ce “sai da maharan suka fito da daliban waje kafin suka buɗe musu wuta.”
Wani dan banga a garin Geidam ya bayyana cewa wani dalibi da ya tsallake rijiya da baya a harin ya samu raunuka kuma yana samun kulawa a asibiti.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilinmu a safiyar Juma’a.