‘Yan bindiga sun kai farmaki a yankin Odu a Jihar Nasarawa inda suka kashe basaraken yankin da tsakar daren Laraba 31 ga watan Yuli.
Maharan da suka zo da yawan gaske a ranar Babbar Sallah sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi kafin su kashe Dagaci Amos Ewa Obere wanda tsohon hafsan dan sanda ne.
“Da suka zo sai suka wuce kai tsaye zuwa fada suka jawo basaraken suka ce masa kwananka ya kare kafin su harbe shi. Kafin mutane su zo su ga abin daya faru, har sun tsere,” inji shi.
Ya ce basaraken ya rasu ne sakamakon raunin bindigar da ya samu a cikinsa, a hanyar kai shi Babban Asibiin da ke Mararraba Udege.
Tsohon shugaban Kungiyar ’Yan Jari ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Nasarawa, Joel Opaga, wanda dan asalin yankin ne ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce abun tikaici ne.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga Shugaban Karamar Hukumar ta Nasarawa, Mohammed Otto da kuma Kakakin ’yan sandan jihar, Rahman Nansel amma duk wayoyinsu ba sa shiga.