’Yan daba sun kai farmaki Fadar Etsu Nupe na Lokoja, Mai Martaba Emannuel Akamisoko Dauda-Sekila, Nyamkpa na Hudu a fadarsa, inda suka kona motoci da kadarori.
Da misalin karfe 1 da dare ranar Asabar ne maharan suka kutsa cikin fadar a cikin wata mota suka yi kone-kone, amma basaraken ya tsallake rijiya da baya.
Ya bayyana cewa dukan kofar fadarsa da maharan suka yi ne ya tashe shi daga barci, “ina fitowa sai na ga an cinna wa motata wuta, na san cewa hari aka kawo, nan da nan sai na fita ta kofar baya domin tsira da rayuwata.”
Ya ce duk da kokarin makwabta na kashe wutar, sai da ta kone motocinsa da sauran dukiyoyi da ke fadar.
- Ma’aikatun da Tinubu ya rushe sun samu N2.4tr a Kasafin 2025
- Jerin mace-mace a wurin turereniyar abincin tallafi a Najeriya
Basaraken ya bukaci gwamnati da jami’an tsaro su bincika lamarin tare da hukunta masu hannu a ciki.
Ya kuma yi kira ga ga al’ummar Nupawa mazauna garin Lokoja da suka kasance masu bin doka kada su dauki doka a hannunsu da sunan ramuwar gayya ko makamancinsa.
An kai mummunan harin ne a yayin da al’ummar Nupawa mazauna Lokoja ke shirin gudanar da bikin ranar Nupawa a garin karo na biyu a ranar 21 ga watan nan na Disamba, 2024. Harin ya sa an dage bikin wanda ke tara al’ummar Nupawa daga wurare daban-daban.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, SP William Aya a kan lamarin, amma har bai samu jami’in ba.