✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kai hari ana tsaka da cin kasuwa a Katsina

’Yan bindigar sun kai hari yankin ana tsaka da cin kasuwa

’Yan bindiga sun kai hari ana tsaka da cin kasuwa a garin ’Yan Tumaki da ke Karamar Hukumar Dan-Musa a Jihar Katsina, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 3:00 na yammacin Juma’a, yayin da jama’a ke tsaka da yin hada-hada.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida wa Aminiya cewar, jami’an tsaron da ke yankin ba su kai musu dauki ba, lokacin da ’yan bindigar ke tsaka cin karensu ba babbaka.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Katsina ta dage dokar hana hawa babura masu kafa biyu a Jihar.

Gwamnatin dai ta ce ta yi hakan ne albarkacin azumin watan Ramadan da al’ummar Musulmai za su fara a karshen makon nan.