Mutum daya ya rasu bayan an yi garkuwa da wasu biyu a harin da ’yan bindiga suka kai kauyen Gidan-Kwano, da ke makwabtaka da Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT) da ke Minna, Jihar Neja.
Majiyoyi sun ce maharan sun kai farmakin ne a daidai babbar kofar shiga jami’ar, wadda wasu dalibanta ke da dakunan kwanansu a unguwar da ke makwabtaka da ita.
- Buhari ya roki Ganduje filin gina tashar wutar lantarki a Bichi
- Nnamdi Kanu zai yi bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara a hannun DSS
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar cewa maharan sun kai farmakin ne kafin wayewar garin ranar Alhamis, amma bai ce komai ba game da mutuwar da aka samu.
Kakakin rundunar ya ce, “Da misalin karfe 11 na dare wasu ’yan daba suka kai hari a wani shago da ke Gidan-Kwano daura da kofar FUT Minna suka kuma sace ’ya’ya biyu na mai shagon.
“Nan take ’yan sanda da ’yan danga suka je wurin inda suka bi sawun bata-garin suka kuma yi nasarar kama daya daga cikin wandanda ake zargin a kauyen Barkuta,” a cewar sanarwar da ya fitar.