’Yan bindiga sun kashe ’yan banga 17 a garin Dukku da ke Karamar Hukumar Rijau ta Jihar Neja.
Wani shaida y ace ’yan bindigar sun harbe ’yan bangar ne a lokacin da ’yan bangar ke kokarin fatattakar su daga garin da suka kai hari.
Maharan sun far wa garin a kan babura kusan arba’in suna ta harbe-harbe.
Ya ce bayan harbe-harbe a dajin da ’yan bangar suka bi sawun maharan ne aka kashe biyu daga cikin ’yan bindigar da kuma ’yan banga 17.
’Yan bindigar sun lashi takobin kin bari a dauki gawar ’yan bangar daga cikin jejin ba, kamar yadda ya ce.
Kwamishinan Wata Labaran Jihar Neja, Muhammad Sani Idris ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce babu tabbacin yawan wandanda aka kashe.
Ya ce gwamantin jihar na daukar sabbin matakai domin wanzar da tsaro a jihar.
Kwamishinan ya ce jihar na kuma ta’aziyya kan harin ’yan bindidga a agarin Kagara da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar.
Muhammad Sani ya bukaci ’yan Kagara da su kwantar da hankalinsu domin gwamnatin jihar na daukar matakan tabbatar da tsaro a yankin.