Mutum 55 sun kwanta dama a wani harin ’yan bindiga a yankin Tilleberi na Jamhuriyar Nijar.
Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwana uku daga ranar Laraba saboda rasuwar, sakamakon harin na ranar Litinin a yankin Tilleberi mai makwabtaka da iyakar kasar Mali.
- Dalilin haramta sinadaran karin dandano a Kano
- Ba ruwanmu da lallashin ’yan bindiga —El-Rufai
- Boko Haram ta kona asibiti da makaranta a Yobe
- An yi wa sojojin da Boko Haram ta kora a Marte afuwa
Majiyoyi sun ce maharan sun yi luguden wuta ne a kan fasinjoji da ke hanyarsu ta komawa gida daga kasuwa sannan suka cinna wa motar wuta.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayane game da maharan, sai dai mayakan jihadi na Boko Haram, ISWAP da dangoginsu sun addabi yankin Sahel.
Ko a watan Janairu sai da aka kashe aƙalla mazauna wani ƙauye 100 a wani harin Jihadi.
(Daga BBC)