✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mahaifiyata ke yi min tsafi in samu nasarar fashi’

Sai dai mahaifiyar ta musanta zargin dan nata

Jami’an Tsaro na Amotekun a Jihar Ondo sun kama kananan yara uku masu suna Timilehin mai shekara 12 da Sunday mai shekara 16 da Odeyemi mai shekara 20 da ake zargi da yin fashi da makami a kauyen Ijare a Karamar Hukumar Ifedapo da ke Jihar.

Da yake nuna yaran ga ’yan jarida a ofishinsa a Akure, Kwamandan Hukumar Amotekun, Mista Adetunji Adeyeye, ya ce Timilehin ya tabbatar da cewa, mahaifiyarsa ce take taimaka masa da tsafi don samun nasara da kariya a duk lokacin da yake gudanar da danyen aikin.

Sai dai mahaifiyar mai suna Iyabo da take tsare ta musanta bayanin dan nata.

Ta ce, ta taba kai shi zuwa wani coci inda wani Fasto ya ba ta sabulun da take yi wa yaron wanka a cikin wani kogi domin kawar da shaidanci a cikin jininsa da shi ke ingiza shi ga yin takadaranci.

Kwamandan, ya ce, “Dukkan yara ukun sun yi wa kansu lakani da sunayen fitattun ’yan fashi irin su Anini da Oyenusi da Osumbo da mahukunta a zamanin mulkin soja suka harbe su a bainar jama’a, bayan yanke hukuncin kisa da kotuna suka yi.

“An samu bindigogi da albarusai da wayoyin salula da kudade a hannun yaran.

“Wadannan yara suna daga cikin mutum 19 da Rundunar ta kama da zargin aikata laifuka a jihar. An taba kama Timilehin da irin wannan laifi a bara inda aka mika shi ga cibiyar gyaran hali ta kangararrun yara, daga baya aka sallame shi saboda karancin shekarunsa.

“Amma yanzu za mu nemi shawarar ma’aikatar shari’a ne. Ita kuwa mahaifiyarsa za mu gurfanar da ita gaban kotu ne.” In ji shi.