✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Maryam Booth ta rasu

Zainab Booth ta rasu bayan watanni da aka yi mata aiki a kwakwalwa.

Rahotanni daga Jihar Kano sun ce Allah Ya yi wa jarumar fina-finan Kannywood, Zainab Booth rasuwa.

Wata makwabciyarsu da ke zaune a unguwar Hausawa Court Road ce ta tabbatar da hakan yayin zanta wa da Aminiya.

Kazalika, Ali Nuhu, daya daga jarumai a Kannywood ya inganta rahoton cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, ALLAH ya yi wa Haj. Zainab Musa Booth rasuwa.

“Gobe za a yi jana’iza a gidanta da ke kallon Premiere Hospital a Court Road da karfe takwas na safe (8:00am).

“ALLAH ya jikan ta da rahama, Ya sa Aljanna ce makomarta,” amin, a cewar sakon.

Marigayiyar ita ce mahaifiya ga Maryam Booth da Amude Booth, wadanda suna daga fitattun jaruman Kannywood da har yanzu tauraruwarsu take haskawa.

Zainab Booth wacce aka dauki tsawon lokaci ana damawa da ita a masana’antar Kannywood, ta rasu bayan wata doguwar jinya da ta danganci kwakwalwa.

A watannin bayan ne aka yi mata tiyata bayan wani bangare a cikin kwakwalwarta ya daina aikin isar da sako zuwa wasu sassan jikinta.