✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin wakilin Aminiya na Jihar Filato ya kwanta dama

Allah Ya yi wa Malam Amadu Isiyaku mahaifin wakilin jaridar Aminiya na Jihar Filato, Hussaini Isah rasuwa. Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar da…

Allah Ya yi wa Malam Amadu Isiyaku mahaifin wakilin jaridar Aminiya na Jihar Filato, Hussaini Isah rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar da ta gabata a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna bayan ya yi doguwar jinya. Ya rasu yana da shekara 75, inda ya bar ’ya’ya hudu da jikoki 15. 

Daga cikin ’ya’yan da ya bari akwai wakilin jaridar Aminiya na Jihar Filato, Hussaini Isah, kuma an yi jana’izarsa a garin Saminaka, kamar yadda addinin Musulunci ya tsara.