Wata mata mai suna Blessing Amuson, ta bukaci kotun Kwatomari da ke zama a Ibadan ta kashe aurenta da mijinta saboda zagon kasa da mahaifinsa yake wa auren nasu.
A jawabinta, Amuson da ke zama a unguwar Apata ta garin Ibadan ta ce, “Mahaifin mijinta ya hana shi ya nuna mani soyayye kamar da.
“Kafin mu yi aure, na samu aiki a Legas kuma muka yi yarjejeniyar zan ci gaba da aikina bayan aure.
“Bayan mun yi aure, sai ya sauya ra’ayinsa ya ce na ajiye aikin in zauna a Ibadan.
“Duk lokacin da yake wajen iyayensa, sai sun canja mashi ra’ayi su kuma ce ya sake ni.
“Wata rana na koma gida na tarar ya canja kubar kofar gidan, na kasa shiga gidan.
“Da na kira shi sai Babatunde ya ce mani mahaifinsa ne ya umarce shi da ya yi haka kuma kar na kara zuwa gidansa.
“Mahaifana sun kira shi har sau uku amma ya ki daukar wayarsu.
“Iyayensa kuma sun ki daukar wayarsu domin a sasanta matsalar da ke faruwa”, inji Blessing.
Mijinta, wanda mahaifin sa, Johnson, ya wakilce shi ya karyata zargin.
Johnson ya ce dansa ya yi tafiya, “Matar nan da iyayenta suka haifar wa kansu wannan matsalar.
“Allah Ya sani ban taba ce wa dana ya Kule ta waje ba.
“Dana ya gaji da yi masa yawo da hankali da take yi ne. Ta ki yarda ta dauki ciki da cewar sai ta kammala bautar kasa sa’anan.
“Ya kamata a ce ma’aurata na tarayya da juna amma mahaifiyarta ta mara mata bata.
“Rayuwarta baki daya ba ta mai aure ba ce. Sutura mai nuna tsiraici take sanyawa duk da cewar mahaifinta malami ne”, inji Johnson.
Da take martani, mahafiyar Amuson ta karyata zargin da aka yi wa diyarta.
“Bai kamata surukin diyata ya tsoma baki cikin rayuwar auren yara ba. Ya daina shiga sabgarsu”, inji ta.
Da zai yanke hukunci, Alkali Henry Agbaje, ya umarci Babatunde ya gurfana gaban kotun.
Ya kuma shawararci mahaifan nasu su zauna lafiya da juna kafin ya dage saurarar karar zuwa 21 ga watan Satumba, 2020.