✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin Mbappe ya fara tattaunawa da kulob din Real Madrid

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Faransa sun ce mahaifin dan kwallon gaba a kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa Kylian Mbappe tare…

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Faransa sun ce mahaifin dan kwallon gaba a kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa Kylian Mbappe tare da dillalin dan kwallon Wilfried sun shiga tattaunawa da mahukunta kulob din Real Madrid da ke Sifen kan yiwuwar saye dan kwallon a karshen kakar wasa ta bana.

Mbappe wanda kulob din Madrid ya dade yana zawarci bayan da Cristiano Ronaldo ya bar kulob din alamu sun nuna zai koma Madrid a karshen kakar wasa ta bana kamar yadda rahoton da kafar labaran wasanni ta Sky Sport ta kalato a shekaranjiya Laraba.

Kafar labaran wasanni ta Sun Sport da ke Ingila ma ta kalato cewa Mbappe ya fara tunanin barin kulob din PSG bayan da kulob din Manchester United da ke Ingila ya fitar da su a gasar cin Kofin Zakarun Turai inda hakan ya kawo karshen burin dan kwallon na lashe wannan kofi a kulob din PSG.

A gasar rukuni-rukuni na Faransa (Ligue 1) a bana, Mbappe dan shekara 20 ya samu nasarar zura kwallaye 26 a wasanni 26 da ya yi sannan ya taimaka wajen zura kwallaye 6 wanda hakan ya sa tauraruwarsa ke haskakawa.

Masana harkar kwallo sun yi hasashen akwai yiwuwar dan kwallon ya canja sheka musamman ganin yadda kulob din Madrid ya sake daukar Zinedine Zidane a matsayin koci bayan kulob din ya ware masa Fam miliyan 240 (kimanin Naira biliyan 113 da miliyan 400) don cefano zaratan ’yan kwallo a karshen kakar wasa ta bana.

Da alama kulob din Madrid zai tashi a tutar babu a kakar wasa ta bana bayan ya rasa damar lashe kowane kofi.