✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uba ya nemi a yi wa dansa daurin rai da rai a Kano

Mahaifin ya nemi kotun ta daure dansa har illah ma sha Allah.

Wani mahaifi  ya yi karar dansa a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke  zamanta a Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano bisa damun sa da ya yi da sace- sace da kuma shaye-shaye.
Mahaifin wanda aka boye sunansa ya nemi kotun ta daure dansa har illah ma sha Allah.
Mai gabatar da kara, Abdul Wada, ya karanta masa kunshin  tuhumar inda nan take  ya amsa laifinsa.
Alkalin kotun,  Mai Shari’a  Malam Umar l Lawan Abubakar, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Yuni 2024 don yanke hukunci.