✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai

Majalisar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan barazanar rarrabawa da sayar da magunguna da kayayyakin abinci na jabu,

Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu.

Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki.

Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan barazanar rarrabawa da sayar da magunguna da kayayyakin abinci na jabu, marasa inganci ko waɗanda wa’adin aikin su ya ƙare a ƙasar.

Yayin da yake gabatar da ƙudirin a zauren majalisar, ya ce ƙaruwar sarrafa da shigo da kayayyaki na jabu da marasa inganci da magunguna da abinci da abubuwan sha a faɗin Najeriya na haifar da babbar barazana ga lafiyar al’umma, tsaron ƙasa da kuma tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce, “Kwanan nan Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya NAFDAC ta kama jabun kayan abinci da magunguna da suka kai na sama da Naira biliyan 5 a wani samame da suka kai a kasuwar Cemetery Market da ke garin Aba, Jihar Abia lamarin da ya nuna yadda wannan matsalar ke yaduwa.

“Najeriya na fama da asarar tattalin arziki kusan tiriliyan 15 a duk shekara saboda jabun kayayyaki da marasa inganci, kamar yadda Hukumar Daidaita Ma’auni ta Najeriya (SON) ta ruwaito. Yaɗuwar samfuran jabu ba wai kawai yana kawo cikas ga amincin masu amfani ba har ma yana hana saka hannun jari na gaske a masana’antar abinci da magunguna.