Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce kyaftin din kungiyar, Harry Maguire na da muhimmanci wajen kawo ci gaba a tsakanin ’yan wasa da magoya bayansu.
Ten Hag ya kare Maguire ne yana mai cewa shi jagora ne ga sauran ‘yan wasan tawagarsa, bayan da kuskuren dan wasan bayan na baya bayan nan ya kai su ga ficewa daga gasar Europa a wasan da suka kara da Sevilla.
- Zababben dan Majalisa mai shekara 36 ya rasu
- Kwamishinan Zaben Adamawa ya yi layar zana bayan sanar da sakamakon bogi —INEC
Kuskuren da Maguire ya yi ne ya janyo Sevilla ta ci su kwallo da wuri a wasan da suka yi a Alhamis, wanda aka tashi 3-0, kuma hakan ya janyo mai caccaka.
Sai dai Ten Hag ya ce dan wasan bayan dan kasar Ingila mai shekaru 30, zai ci gaba da zama muhimmin dan wasa a cikin tawagarsa.
Ya ce Maguire yana taka rawa mai mahimmanci a matsayinsa na Kyaftin din kungiyar, saboda yana magana da ‘yan wasa, yana kuma jagoranci ta wajen kara wa musu kwarin gwiwa.
United za ta fafata a wani babban wasa a ranar Lahadi a gasar kofin FA, matakin daf da karshe, inda za ta kara da Brighton a filin wasa na Wembley.