✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidanta 4 sun amsa laifin aikata luwadi da kananan yara a Katsina

Na yi amfani da daya daga cikin yaran sama da sau goma.

A ranar Talatar da ta gabata ce Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina SP Gambo Isa ya gabatar da wasu mutum hudu bisa zarginsu da yin luwadi da wasu yara kanana.

Kamar yadda Kakakin ya ce, “A ranar 14 ga wannan wata na Oktoba, 2020, wani mai suna Haruna Ibrahim na Unguwar Yari, ya kai koke ofishin ’yan sanda da ke Kofar Soro.”

“Haruna ya kai korafi bisa zargin da yake yi wa wani Jamilu Kabir mai shekara 30 da Abubakar Magaji mai shekara 30 da Ilyasu Ya’u mai shekara 51, dukkansu Unguwar Yari, sai kuma Musa Abdulkadir mai shekara 43 na Unguwar Madawaki, cewa suna luwadi da kananan yaransa biyu; Musa mai shekara 16 da kuma Abdurrashid mai shekara 13.”

Aminiya ta samu cewa hakan ya sanya rundunar ’yan sandan ta nemo tare kama wadanda ake zargin.

Kakakin ya ce ababen zargin sun amsa laifinsu, kuma da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.

Daya daga cikin wadanda ake tuhumar Jamilu Kabir ya ce, ya yi amfani da daya daga cikin yaran sama da sau goma, shi kuma yaron ya ce, ya fi sau 20.