Wani mutum mai suna Shane Smith ya firgita lokacin da ya fede wani babban kada mai nauyin dutse 53 (laba 750), inda kuma ya gano wasu tsofaffin abubuwan tarihi wadanda suke tsakanin shekara 5,000 zuwa 6,000.
Ana kyautata zaton kayan dai na tarihi ne da ’yan asalin kasar Amurka suka yi amfani da su a wancan lokaci.
- Ganduje ya nada sabon Sarkin Gaya
- Afghanistan: Taliban ta rataye masu garkuwa a tsakiyar gari a matsayin jan kunne
Mutumin da ya kama babban kadan ne bayan ya ci wasu tsofaffin kayan tarihi wadanda ba a gano su ba tsawon shekara 6,000.
Mafaraucin ya kama kadan ne mai tsawon kafa 13 da nauyinsa da ya kai lamba 750, sannan ya kai wa Shane Smith wanda ya fede kadan tare da wani mafarauci mai suna John Hamilton.
Kadan da yake dauke da kayan tarihin, an kama shi ne a Jihar Mississippi da ke Amurka, kuma an gano kayan ne a cikin cikinsa da suka hada da wata tsohuwar kibiya da mayen karfe, kamar yadda jaridar Daily Star ta ruwaito.
Da farko, sun yi zaton an harbi kadan ne da kibiyar, amma sai suka fahimci cewa kibiyar ta tsufa sosai, kuma wani masanin ilimin kasa ya gano cewa, ’yan asalin kasar Amurkan sun yi amfani da irin wannan kayan tarihin kusan shekara 6,000 da suka gabata.
Wadansu dai sun yi sharhi game da abubuwan da aka gano a cikin kadan, a shafukan sada zumunta kamar Facebook.
Kamfanin Sarrafa Tsirrai na Shane Red Antler Processing, ya wallafa a Facebook: “Mun kasance muna yanka manyan kadoji don ganin abin da yake cikinsu. Amma da ganin wadannan abubuwa da aka samu a cikin wannan kadan kowa ya razana.”
Kadan da John Hamilton ya kawo jami’an sun razana matuka duk da girmansa na tsawon kafa 13 da inci 5.
Masanan tarihi sun ce a karnin da ya gabata an samu nau’o’in kayan kamun kifi da mafarauta ’yan asalin Amurka suka yi amfani da su irin