Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin alherinSa da kaunarSa zuwa gare mu. Barkanmu da sake saduwa a wannan mako.
A wannan makon za mu ga wasu ayoyi ne daga cikin Littafi Mai tsarki domin karfafawa cikin damuwa.
Yau da kullum, muna fuskantar kalubale da damuwa iri-iri a fannoni da dama cikin rayuwarmu. Domin tsananin irin wannan yanayi, mutane da dama sukan manta da alkawarin Ubangiji Allah Mahalicci Mai iko duka. Sukan bi nasu nufi. Duk wani nufi da ba na Ubangiji ba kuwa, yakan kai mutum na ga hallaka.
Idan har muka lura, kalubale da damuwar rayuwa abin tuni ne zuwa gare mu cewa ba za mu iya rayuwar nan da ikon kanmu ba in ba tare da Ubangiji ba, domin Shi ne mafakarmu da cetonmu.
A zamanin da muke ciki yau, duk arziki da ilimi ko iko, har ma zuwa ga talauci, babu wanda zai ce bai taba fuskantar damuwa ba a cikin rayuwarsa. Mun sha ji sau da dama mutane da yawa na bimbinnin yi ko kuma sukan yi kisan kai wai don su rabu da damuwar rayuwar nan, a ganinka sun rabu da ita ke nan? Sam, babu wata hanyar tsira idan ba ta wurin Ubangiji Allah ba.
Ka tuna fa kai kadai ka san irin damuwar da kake ciki, kuma Ubangiji Mahalicinka Ya fi ka sani, kuma Shi Ya san hanyar kubuta daga irin wannan hali, to me zai hana ka mika maSa rayuwarka da kuma irin halin da kake ciki?
Bari mu ga wasu ayoyi (kadan) daga cikin Littafi Mai tsarki da za su karfafa mu a duk lokutan da muka shiga damuwa.
Zabura 9:9: “Ubangiji mafaka ne ga wadanda ake zalunta, Wurin buya a lokatan wahala.”
Maimaitawar Shari’a 31:8, “Ubangiji Kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya.”
Filibiyawa 4:8-9,11-13: “Daga karshe kuma, ’yan uwa, ko mene ne yake na gaskiya, kome ne ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin kauna, ko mene ne daddadar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan wadannan abubuwa za ku yi tunani. Abin da kuka koya, kuka yi na’am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah Mai zartar da salama zai kasance tare da ku. Ba cewa, ina kukan rashi ba ne, domin na koyi yadda zan zauna da wadar zuci a cikin kowane irin hali da nake. Na san yadda zan yi in yi zaman kunci, na kuma san yadda zan yi in yi zaman yalwa. A kowane irin hali duk ana horo da koshi da yunwa da yalwa da rashi. Zan iya yin komai albarkacin wannan da yake karfafa ni.”
Zabura 34:18-19: “Ubangiji Yana kusa da wadanda suka kira Shi, Yakan ceci wadanda suka fitar da zuciya. Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, Amma Ubangiji Yakan cece shi daga cikinsu duka.
2 Samaila 22:17-22: Daga sama Ubangiji Ya miko Ya dauke ni, Ya tsamoni daga zuzzurfan ruwa. Ya kubutar da ni daga wadanda suke ki na, Daga abokan gabana, wadanda suka fi karfina! Sa’ar da nake cikin wahala sun auka mini, Amma Ubangiji Ya kiyaye ni. Ya taimake ni Ya fisshe ni daga hadari, Ya cece ni domin Yana jin dadina.“Ubangiji Ya saka mini bisa ga adalcina, Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin komai. Gama na kiyaye dokar Ubangiji, Ban yi wa Allahna tawaye ba.”
Ishaya 26:3-4: “Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji, Ga wadanda suke rike da manufarsu da karfi, Wadanda suke dogara gare Ka. Ku dogara ga Ubangiji har abada. Zai kiyaye mu kullum.”
Zabura 40:1-3: “Na yi ta jiran taimakon Ubangiji, Sa’an nan Ya kasa kunne gare ni, ya ji kukana. Ya fisshe ni daga rami mai hadari! Ya aza ni a kan dutse lafiya lau. Ya kawar mini da tsoro.Ya koya mini raira sabuwar waka, Wakar yabon Allahnmu. Da yawa idan suka ga wannan za su tsorata, Za su kuwa dogara gaUbangiji.”
Zabura 9:10-11: “Wadanda suka san Ka za su amince da kai, ya Ubangiji, Ba za Ka kyale duk wanda ya zo gare ka ba. Ku yabi Ubangiji, Shi da Yake mulki a Sihiyona! Ku fada wa kowace al’umma abin da ya yi!”
Zabura 25: 3: “Wadanda suke dogara gare Ka, Ba za su kasa yin nasara ba, Sai dai wadanda suke gaggawa su yi maka tayarwa.
Zabura 37:23-24: Ubangiji Yakan bi da mutum lafiya, A hanyar da ya kamata ya bi, Yakan ji dadin halinsa, In ya fadi, ba zai yi warwar ba, Gama Ubangiji zai taimake shi Ya tashi tsaye.”
Romawa 8:38-39: “Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala’iku, ko manyan mala’iku, ko al’amuran yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko, ko tsawo, ko zurfi, kai, ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da kaunar da Allah Yake yi mana ta wurinAlmasihu Yesu Ubangijinmu ba.”
Filibiyawa 4:6-7: “Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roko, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukan fahimta, za ta tsayar da zukatanku da tunaninku ga AlmasihuYesu.”
Bari Ubangiji Allah Ya ba mu zuciyar ganewa, mu kuma dogara a gare shi, amin.