Real Madrid da Gwamnatin Jihar Ribas sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin kai don inganta wasanni tsakanin yara da matasa a Kwalejin Real Madrid da ke Fatakwal.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kelvin Ebiri, Mataimaki na Musamman kan harkokin Yada Labarai ga Gwamnan Jihar Ribas.
- Sarkin Musulmi ya cika shekara 15 a kan mulki
- PSG za ta raba gari da Ramos, Tottenham za ta dauki Conte
Kamar yadda Gidan Rediyon Faransa RFI ya ruwaito, sanya hannu kan wannan yarjejeniya ya gudana ne tun a watan Oktoban da ya gabata a dakin taro na Real Madrid Sport City, da ke Madrid na Spain.
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a madadin Gwamnatin Jihar Ribas da Mista Enrique Sanchez, Mataimakin Shugaban Zartarwa, Gidauniyar Real Madrid da Mista Jihad Saade, Shugaba, Interact Sports, ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.