✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madarar sukudaye ta kashe matashi a Nyanya

  Wani matashi makaniken mota mai suna Bashir Hassan a garin Nyanya, Abuja ya rasa ransa bayan ya sha madarar sukudaye don ya yi maye.…

 

Wani matashi makaniken mota mai suna Bashir Hassan a garin Nyanya, Abuja ya rasa ransa bayan ya sha madarar sukudaye don ya yi maye. Wani abokin sana’ar mamacin mai suna Abdulkarim Ibrahim ya shaida wa Aminiya cewa marigayin wanda dan asalin garin Gombe ne, ya ce sun yi aiki da shi a ranar Alhamis din makon jiya ranar da ya rasu har zuwa maraice da suka tashi ba tare da ya nuna alamar rashin lafiya ba.

Ya ce, “Bayan Sallar Magariba sai na kula da yanayinsa na nuna ya sha kayan mayen saboda yana zazzare ido. Da misalin karfe 11:30 na dare sai a ka tayar da ni daga barci cewa wane ya rasu. “Duk kokarin da muka yi a baya don ya daina shan sukudayen bai samu nasara ba. Ta yi masa illa mai alamar kuna a hannu da duk inda ta diga a jikinsa daga ledar da yake sha wanda idan mutum bai sani ba sai ya dauka kuna ne ta salansar inji ko na wani abu daban.”

Sarkin Hausawan Nyanya Alhaji Musa Muhammad Dala ya ce bayan sun tuntubi iyayen mamacin, an yi masa jana’iza washegari Juma’a tare da wasu daga cikin danginsa da ke Abuja, sai dai ya ce ba su sanar da ofishin ’yan sanda ba da lamarin kasancewar da farko an lullube musabbabin rasuwarsa aka dangantata da ciwon ciki sai daga baya suka samu cikakken bayanin abin da ya yi masa ajali.