✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maciji ya haɗiye wata mata a Indonesia

A bara, mazauna yankin sun kashe wani maciji da ya shake wani manomi yana kokarin hadiye shi.

An gano gawar wata mata mai suna Farida a cikin wani maciji bayan ya hadiye ta a kasar Indonesiya, kamar yadda wani jami’i ya sanar.

Mijin Farida mai shekara 45 kuma mazauna kauyen Kalempang da ke Lardin Sulawesi ta Kudu ya gano ta a cikin wani maciji jinsin mesa da aka auna tsawonsa da ya kai mita biyar (kafa 16).

Farida wadda mahaifiyar ’ya’ya huɗu ce, ta bace a wata ranar Alhamis da dare, kuma ta kasa komawa gida, lamarin da ya sa aka shiga nemanta, kamar yadda Mai garin kauyen, Suardi Rosi ya shaida wa kafar yada labarai ta AFP.

Mijinta “Ya rasa matarsa… wanda ya sa shi shakka. Daga nan mutanen kauyen suka fara bincike. Ba da dadewa ba suka hango wani maciji mai katon ciki,” in ji Suardi.

Ya ce, “Sun amince a fede cikin macijin. Da suka yi haka, sai ga kan Farida ya ya fito.”

An iske Farida sanye da suturarta a cikin macijin. Ana ganin irin wannan lamari ba kasafai ke faruwa ba, amma mutane da dama sun mutu a kasar Indonesiya a ’yan shekarun nan bayan gano cewa macizai na hadiyr mutane.

A bara, mazauna Gundumar Tinanggea a Sulawesi ta Kudu maso Gabas sun kashe wani maciji mai tsawon mita takwas, wanda aka same shi ya shake wani manomin kauye yana kokarin hadiye shi.

A shekarar 2018, an tsinci gawar wata mata mai shekara 54 a cikin wani maciji mai tsawon mita bakwai a garin Muna da ke Kudu maso Gabashin Sulawesi.

Kuma a bara wani manomi a yammacin Sulawesi ya bace kafin a same shi da ransa bayan maciji ya raunata shi a wata gonar manja.