Wani dan kasar Indiya mai suna Mujahid mai shekara 20 ya yi zargin cewa an yi masa tiyatar canjin jinsi zuwa mace ba tare da izininsa ba, bayan da wani mutum ya shirya hakan don ya aure shi.
Mujahid dan asalin kauyen Sanjak da ke Jihar Uttar Pradesh labarinsa ya karade kasar Indiya bayan da ya yi zargin cewa wani abokin hamayyarsa ne ya yaudare shi ya kai shi Asibitin Kwalejin Kiwon Lafiya na Begrajpur da ke Mansoorpur, inda likitoci suka yi masa tiyata cikin yaudara suka canza jinsinsa ba tare da yardarsa ba.
Mutumin ya shaida wa hukumomin kasar cewa wani mutum mai suna Omprakash ya yaudare shi cewa yana fama da matsananciyar rashin lafiya, sannan ya yi tayin kai shi Asibitin Mansoorpur domin a yi masa magani.
- Dalilai uku da ke janyo rikici tsakanin ’yan siyasa da sarakuna
- ’Yan ta’adda sun tsere daga gidan yarin Nijar
Mujahid ya ce jim kadan da isa asibitin ne aka kwantar da shi sannan wasu likitoci da suka hada baki da Omprakash suka yi masa tiyata.
Washegari da ya farka, aka ce masa shi ba namiji ba ne, mace ce yanzu.
“Ya kawo ni nan, sai da safe aka yi mini tiyata. Da na dawo hayyacina, sai aka ce min an canza min jinsin halittata daga namiji zuwa mace,” Mujahid ya shaida wa manema labarai na kafar yada abarai ta NDTV.
“Lokacin da na farka, Omprakash ya gaya mini cewa ni mace ce yanzu kuma zai kai ni babban birnin Lucknow na jihar don ya aure ni.
“Ya yi barazanar kashe mahaifina idan na bijire masa.”
Mujahid ya yi zargin cewa Omprakash ya shafe shekara biyu yana takura masa a yunkurinsa na kwace masa filayen iyalansa, kuma wannan dabarar da ya yi masa mai ban tsoro na nufin tilasta wa Mujahid aurensa domin ya samu damar kwace filin da yake so ba bisa ka’ida ba.
Ya zargi likitocin Asibitin Kwalejin Begrajpur Medical College da aiki tare da Omprakash, sai dai ma’aikatan asibitin sun nace cewa an yi masa tiyatar canjin halittarsa ce da son ransa.
Ya ce Omprakash ya shaida masa cewa, ‘Na canza ka daga namiji zuwa mace, kuma yanzu dole ne ka zauna tare da ni. Na shirya mana lauya don yin aure a kotu.”
Mujahid ya Omprakash, ya gargade shi cewa babu wanda zai yarda da shi a matsayin namiji a yanzu ko da danginsa ne.
Ya ce ya shaida min cewa, “Zan harbe mahaifinka kuma za a sa sunan wanda zai gaji filinsa da sunana sannan in sayar da shi in tafi birnin Lucknow.”
’Yan sanda sun fara bincike tare da kama Omprakash, wanda ya ci gaba da musanta tuhumetuhumen da ake yi masa.
Kuma game da ma’aikatan asibitin suna bincike kan lamarin, amma har yanzu akwai bayanai da dama da za a fayyace, kamar dalilin da ya sa Mujahid ya je asibitin da wani mutum da ya ce ya shafe shekaru yana takura masa.