✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mace mai kai wa ’yan bindiga kayan abinci

Ta kai jami'an tsaro gidan shugaban ’yan bindiga da ake nema ruwa a jallo

’Yan sanda sun kama wata mata da take kai wa ’yan bindiga kayan abinci da sauran bukatun yau da kullum.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Benedict ya yi holen matar mai ahekaru 47 ne bayan an kamata a cikin daji a yankin Jihar Neja.

Ta bayyana cewa tana kai wa ’yan bindiga kayan abinci da sauran bukatun yau da kullum.

Ya bayyana cewa matar ta shaida musu cewa ta yi jigilar kayan abinci ga daya daga cikin kungiyar ’yan bindiga da ke karkashin jagorancin dan ta’adda Shumau, wanda ake nema ruwa a jallo.

Ya ce an kama matar ne a Dajin Gidan-Dogo a lokacin da take kokarin kai wa ’yan bindiga kayan abincin.

Bayan kama ta, ta jagoranci ’yan sanda zuwa gidan Shumau, inda aka kwato shanun sata 14.