Hajiya Inna Galadima ta jam’iyyar APC, ta zama Shugabar Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno.
Aminiya ta ruwaito cewa Hajiya Inna, ta zama mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar karamar hukuma a tarihin Jihar Borno.
- Mutum 16 sun mutu a hatsarin mota a hanyar Kano-Kaduna
- Sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga a Kaduna
Hajiya Inna, ta taba rike mukamin kwamishina da kuma mukamin mai bai wa gwamnan Borno, shawara ta musamman.
Kafin Hajiya Inna Galadami, shugabar karamar hukuma mace ta farko a Jihar Borno ita ce Fanta Baba Shehu, wadda da farko aka zabe ta mataimakiyar shugabar karamar hukuma a tsohuwar jam’iar UNCP, amma daga bisani ta zama shugabar karamar hukuma ta hau kujerar sakamakon rasuwar ciyaman din.
A ranar Lahadi ne, Shugaban Hukumar Zabe na Jihar Borno, Farfesa Mohammed Konto, ya ayyana Hajiya a matsayin wadda ta lashe zaben Karamar Hukumar Jere a jihar.
Konto, ya ce ta samu kuri’u 110,459, inda ta doke abokin hamayyarta na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 2,478.
Jam’iyyar APC mai mulki a jihar, ta lashe zaben kananan hukumomin jihar 27 da na kansiloli 312 da ke jihar baki daya.