✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mace ta kai ƙarar mijinta saboda rashin wanka da wanke baki

Yana wanka sau daya duk mako guda zuwa kwana goma, kuma yana wanke baki sau daya ko sau biyu a mako.

A kwanan ne wata mata mai suna A.Y. ‘yar kasar Turkiyya ta kai karar mijinta, inda ta ce ba kasafai yake yin wanka ba, yana ikirarin cewa yana yin wanka, amma duk da haka yana warin zufa, sannan yana wanke hakoransa sau daya ko sau biyu a mako.

Matar mai suna A.Y. a kafar yada labaran kasar Turkiyya ta tattara rahoton shigar da karar mijinta mai suna C.Y da laifin rashin tsaftar jikinsa a matsayin babban dalili.

Lauyan wadda ta shigar da karar ya shaida wa Kotun Iyali ta 19 da ke Ankara cewa, wanda ake tuhuma yana sanya tufafi iri daya ne akalla kwanaki 5 a jere, ba kasafai yake wanka ba, kuma kullum ya kasance cikin gumi sai warin zufa ya rika tashi.

An kawo shaidu don tabbatar da wadannan ikirari, ciki har da abokansa da ma wasu abokan aikin mijin.

Dukkansu sun ba da bayanan da ke tabbatar da rashin tsaftar mutumin, wanda ake tuhuma.

Kotun ta amince da bukatar matar na saki sannan ta kuma umurci mijin da ya biya matar kudin kasar Turkiyya na Lira 500,000 na Turkiyya, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 14 da dubu dari bakwai da dubu 92 da dari 250, (N14,792250.00) a matsayin diyya saboda jure rashin tsafta.

Lauyan A.Y, mai suna Senem Yılmazel, ya shaida wa jaridar Sabah ta Turkiyya cewa, “idan rayuwar auren da aka raba ta zama ba za a iya jurewa ba saboda halayyar mutum daya daga cikin ma’auratan yana da hakkin ya shigar da kara.

“Dole ne mu yi taka-tsantsan a cikin yanayin dangantakar dan Adam! Don haka, dole ne mu mai da hankali ga dabi’unmu cikin yin tsafta.”

A cikin dokokin farar hula na Turkiyya, dalilan da aka yarda da su na raba aure sun kasu kashi biyu – dalili na musamman da kuma dalili na gaba daya – tare da duk biyun da suka hada da duk dalilan da ke sa daya daga cikin ma’auratan ba zai iya jurewa ba ko duka biyun.

A cikin wannan lamari na musamman, rashin tsaftar miji ya kasance daya daga cikin hujjar raba aure da Kotun Shari’a ta Yankin Kasar da Kotun Koli ta daukaka kara, wanda hukuncin kwanan nan ya kasance na karshe.

Takardun kotun sun nuna cewa, a cewar shaidun da suka tabbata, mijin matar mai suna C.Y. yana wanka sau daya ne a mako guda zuwa kwana goma, kuma kawai yana wanke hakoransa sau daya ko sau biyu a mako, wanda hakan ya sa bakinsa ke yin wari, “abin da ba za a iya jurewa ba”.

Abin sha’awa, wasu abokan aikin mutumin sun yarda su bayyana a matsayin shaidu a cikin wannan kara da ake saurare kuma sun bayyana cewa, warin jikinsa ya sa yin aiki tare da shi ke da wuya matuka.

Ana yin amfani da rashin tsaftar mutum a matsayin dalilin raba aure a da. Idan ba za aiya manatawa ba, a 2018 mun yi rahoto game da wani mutumin Taiwan da ya saki matarsa saboda tana wanka sau daya kawai a shekara, kuma bayan shekara uku mun ba da labarin wani Ba’indiye da ya yi kokari ya saki matarsa saboda ba ta yin wanka a kullum.