Assalamu alaikum. Barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili. Ganin watan Ramadan ya gabato, yau za mu fara gabatar da ayyukan da suka kamata a gabatar kafin kamawar watan. Da fatan Allah Ya amfanar da mu baki daya, amin.
1. Kyauatata Niyya: Abu na farko, kuma mafi alfanu, shi ne ma’aurata su daura kyakykyawar niyyar cin ribar wannan muhimmin lokaci don dacewa da dukkan alheran da ke cikinsa. Za su yi haka ne ta hanyar kudirta wa ransu dagewa wajen yin dukkan ayyukan ibada da na kyautatawa don su samu dacewa da rahama da gafarar da Allah Ya yi tanadi ga bayinSa da suka aikata kyawawan ayyuka a cikin wannan wata. Haka kuma in ma’aurata suka kudirta wa kansu yin ayyukan alheri cikin wannan wata, wannan zai kara musu taushin zuciya ya kuma bude musu hanyar karuwar imani. Kamar yadda Annabi (SAW) ya sanar mana cewa dukkan ayyuka ba su tabbata sai da niyya, don haka duk wani aikin da ma’aurata ke son aiwatar da shi cikin Ramadan, to sai su fara da kulla masa kyakykywar niyya tun yanzu, kuma su tabbatar da niyyar nan cikin zuciyarsu, sannan su yi ta kara jaddada wa kansu wannan niyya, koda ta hanyar rubutawa a takarda don karantawa kullum har sai wannan niyya ta zama babba kuma sanannen kudiri a cikin zuciyarsu. Wannan zai zama garanti gare su na cewa lallai in Ramadan ya tsaya, to za su samu nasarar aiwatar da dukkan ayyukan alherin da suka yi niyya. Haka kuma ma’aurata suna iya rubuta kudirorin da suke son cimma aiwatar da su cikin Ramadan a takarda, tare ko daban-daban, sai su rika yawan karanta su don jaddada su cikin ma’aikatar hankalinsu.
2. Shirya Zuciya: Ta hanyar yawan karanta ayoyin Alkur’ani safe da maraice, yin kyakykyawan tuba daga laifuffukan da mutum ya aikata; yawan kyauta da yin sadaka ga mabukata; gyara zuciya da kawatata da ayyuka masu kyau, raya ta da yawan tunanin Allah da kyautata zato gare Shi da kuma guje wa aikata ayyukan sabon Allah da munana zato ga Allah (SWT), duk ayyukan da ke kusanta bawa ga Ubangijinsa ne wadanda tun kafin Ramadan ya kamata a fara gabatar da su ba lallai sai cikin Ramadan kadai ba, zuciyar mumini mai bukatar Ubangijinta ne a kowane lokaci.
3. Shirya Muhalli: Babban bako, mai matukar muhimmanci zai bakunci gidanku ya ku ma’aurata! Don haka yana da matukar muhimmanci ku yi dukkan shirin da ya kamata don yi masa tarba mai kyau da ba shi mafi kyan masauki a cikin gidan. Don tabbatar da haka, sai ku yi amfani da wadannan hanyoyi:
*Kwana biyu ko uku kafin Ramadan, sai a share gida gaba dayansa, a cire yana, a kwashe kwata; a rage tarkace, mai sauran amfani a kyautar ga masu bukata, marasa amfani a zubar a bola; sannan a rage like-like da kayan kawa, musamman hotuna da like-liken kwalliya masu daukar hankali lokacin ibada; sannan a gyara wuraren da siminti ya farfashe musamman in ruwa na yawan kwanciya a wurin; in kuma fentin gidan ya tsufa, kuma in da halin yin sabo, to sai a yi ga duka ko wani bangare mafi muhimmanci na gidan.
* A tanadi hanyar samun ruwan amfanin yau da kullum, kuma a tanadi hanyoyin samun haske da daddare.
* A tabbatar cewa murhun da ake amfani da shi, na itace, risho ko na gas, bai da wata matsala, in kuma yana da matsala a yi kokarin gyarawa kafin Ramadan. Sannan a tanadi makamashin konawa, wato itace, kananzir ko gas daidai gwargwadon hali.
* A tanadi dukkan kayan abinci daidai gwargwadon hali, sannan masu bukatar gyara sai a gyara su yadda da an zo amfani da su cikin Ramadan, kawai sai dai a sarrafa ba sai an tsaya gyarawa ba.
*A yi dukkan saye-sayen kayan Sallah da dinkunan Sallah tun kafin Ramadan, ta yadda in watan ya tsaya sai dai a mai da hankali wajen ibada da bautar Allah kadai.
* A kaurace wa kallon talabijin ko sauraron kade-kade, sai na shirye-shiryen addini kadai; in kuma har ya kasance garin kallonsu za a kunno wasu tashoshin wasannin banza, to sai a dauke talabijin din gaba daya daga wajen kallon har sai bayan Ramadan.
4. Gyara dangantaka: Yana da kyau ma’aurata ku yi dukkan kokari na gyarawa da inganta dangantakarku kafin isowar watan Ramadan. Da haka ne za ku dace da cin ribar dukkan alheran da ke cikinsa. Ku yi kokarin kara kusanci da shakuwa da juna da kuma kara karfafa zumuncin auren da ke tsakaninku. Karin kyautatawa ga juna, karin yin hakuri da juna, da sauran kyawawan abubuwa na dadada wa juna. Ku zauna ku tattauna game da dangantakarku, ku yi afuwa ga juna, ku toshe duk wata baraka da ke tsakaninku don ya kasance in Ramadan ya zo, ba abin da ke gabanku sai more rahmar da ke cikinsa da yin ibada.
Allah Ya sa mu dace da dukkan ni’imomin wannan wata mai albarka, amin.