A safiyar ranar Litinin ne ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO suka rufe ofishinsu saboda zargin ba a shigar musu da kudin fanshonsu da ake yankewa daga albashinsu na tsawon watanni 72.
Ma’aikatan karkashin inuwar Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) sun yi alkawarin cewa ba za su bude kamfanin ba har sai an shigar musu da fenshon nasu.
- Balaraben Qatar ya janye tayin sayen Manchester United
- Gwamnati ta bai wa Direbobin Danfo wa’adin daina kasuwanci a kan gadojin Legas
Malam Ado Riruwai shi ne Shugaban kungiyar reshen Arewa maso Yamma, ya bayyana cewa ba za su lamunci wannan dabi’a ta tauye hakki ta ci gaba da faruwa ba.
’Ya’yan kungiyar sun zargi Kamfanin da cin zarafinsu a kan abin da suke yi na kwato hakkin ’yan uwansu ma’aikata tare da yin magana a madadinsu.
“Wannan abu ba daidai ba ne a gana Mai hakki hakkinsa. Don haka ba za mu lamunta ba”
Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin shugabannin kamfanin ya ci tura, kasancewar ’yan kungiyar sun kori dukkanin ma’aikatan da ke cikin kamfanin waje.
Har ila yau, ’ya’yan kungiyar sun zargi Kamfanin da kin kulawa da sha’anin lafiyar ma’aikatan “duk kuwa da hatsarin da aikin nasu yake da shi,” a cewar Ado Riruwai.