Gamayyar kungiyoyin Ma’aikata marasa koyarwa a jami’o’in Najeriya, sun sanar da ranar 5 ga watan Fabrairun 2021 a matsayin ranar da za su gurgunta harkokin karatu a dukkan jami’o’in da ke fadin kasar.
Kungiyoyin da suka hada da na Manyan Ma’aikatan SSANU da kuma kungiyar NASU ta Ma’aikata marasa koyarwa, sun sanar da matakin hakan ne a ranar Juma’a da cewa za su tsayar da harkokin ilimi muddin gwamnati ta ci gaba da watsi da bukatunsu.
- An gurfanar da masu gyara a kotu kan zargin satar mota
- Matashi dan shekara 22 ya kashe kansa a Kaduna
- Sun da Xu: Ma’aurata mafi ya tsawo a duniya
A makon da ya gabata ne kungiyoyin suka gudanar da zanga-zangar lumana ta kwanaki uku domin yi wa gwamnatin matsin lambar ganin ta waiwayi bukatunsu, lamarin da suka ce daga wannan za su dauki mataki na gaba.
Yayin zanta wa da manema labarai a birnin Abuja, Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU), Muhammad Haruna Ibrahim, ya ce sun yanke shawarar hakan ne bayan tattaunawar da suka yi da dukkanin rassansu da ke fadin kasar.
Ya ce, “kashi 90 na mambobin NASU sun amince a shiga yajin aikin sai baba ta gani yayin da kashi 10 suka juya baya a kan hakan.”
Kazalika, ya ce, “kashi 83 na mambobin kungiyar SSANU sun aminta a kan shawarar da aka yanke sannan kashi 11 na adawa da hakan yayin da kashi 6 suka kasance ’yan ba ruwansu.”
“Saboda haka wa’adin makonni biyu da muka dibar wa gwamnatin da sauran masu ruwa da tsaki zai fara ne daga yau, 22 ga watan Janairu,”a cewarsa.
Daga cikin matsalolin da kungiyoyin suke bukatar gwamnatin ta warware akwai takaddamar da ta dabaibaye sabon Tsarin Biyan Albashi na bai daya (IPPIS).
Sauran lamuran da ke ci wa kungiyar tuwo a kwarya sun hada da tsarin raba Naira biliyan 40 na alawus-alwawus a tsakanin ’ya’yanta da na kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU da kuma jinkirin tabbatar da yarjejeniyar bangarori biyun suka kulla tun a shekarar 2009.