Wani ma’aikaci a filin jirgin sama mai suna Richard Russell da yake kula da jakunkunan matafiya ya saci wani jirgin sama na Alaska Airlines a filin jirgi na Seattle da ke Amurka, inda jami’an filin jirgin suka saki bidiyon yadda ya saci jirgin tare da lulawa zuwa sararin samaniya.
A bidiyon an ga yadda Richard Russell ya shiga ma’adanar jiragen saman tare da fito da jirgin inda ya tuka shi ya rika shawagi kafin ya yi hadari a wani tsibiri Russell.
- Adeleke na Jam’iyyar PDP ya lashe zaben Gwamnan Osun
- Ta yaya za a gyara tabarbarewar harkar ilimi a Najeriya?
Ya kwashe awa daya da minti 13 ana rokonsa kan ya sauko kasa, amma ya rika zolayar masu kula da jiragen da yake magana da su.
Hukumomin filin jirgin sun saki bidiyon CCTV daga kyamarorinsu na ciki da wajen filin wanda ya nadi yadda lamarin ya faru.
A bidiyon, matashin Richard Russell mai shekara 29 ya ratsa ta wurin jami’an tsaron filin jirgin sanye da riga mai gajeren hannu.
Bayan sa’o’i biyar, an ga Russell yana shiga wurin da ake adana jirage kuma ya shiga jirgi tare da kama hanyar fita da shi.
Masu kula da tafiyar jiragen sama sun fara gane cewa akwai abin da yake faruwa kuma sun yi kokarin yin magana da wanda ke cikin jirgin amma ba su samu martani ba.
An ga abokan aikin Russell suna kai-kawo a wurin, ba su san ya shiga wurin tukin jirgin ba. An ga Russell ya bude wurin matukan jirgin kuma ya shige mazaunin tare da tuka jirgin ya tashi sama.
Bidiyon da aka nada daga kasa ya nuna yadda yake tafiyar ganganci da jirgin.
“Kai, gani a cikin wani hali. Ina sararin samaniya yanzu haka. Zan yi ta yawo ne kawai,” aka ji Russell yana fada ta rediyon jirgin.
Sautikan muryoyin da aka nada, an ji yadda masu kula da jirgin ke ta kokarin shawo kansa ya sauka. Ana jin yadda Russell ya rika zolayarsu.
A wani lokaci ma, ya tambayi daya daga cikin masu yi masa magana cewa: “Kai kana ganin idan na sauka lafiya Alaska za ta ba ni aikin yi a matsayin matukin jirgin sama?”
Mai kula da jirgin ya yi masa martani da cewa “Eh, ina tunanin za su iya ba ka kowane irin aiki idan ka sauko lafiya.”
Russell ya yi martani da: “Eh gaskiya.” Sai ya ce masa “Akwai wurin sauka nan kusa da kai ta bangaren dama kusan mil daya ne tsakaninku, ka gan shi?”
“A’a wadannan za su yi kokarin hukunta ni idan na sauka a nan inji Russell.
Ya kara da cewa “Kuma ina tunanin zan iya bata wani abu a wurin. Ba zan so yin haka ba. Ko kuma suna da abin harbo jiragen sama.”
“Basu da shi, muna dai kokarin samo maka inda za ka sauka lafiya ne,” mai kula da jirgin ya fada masa.
Russell ya sanar da shi cewa bai shirya sauko da jirgin saman ba.
Jiragen yaki biyu sun tashi daga Portland mintoci kadan bayan tashin jirgin saman domin su tare shi. Sai dai ba su samu nasara ba.
Bayan sa’a daya da minti 13, Russell ya kifar da jirgin da gangan a wani tsibiri, lamarin da ya yi ajalinsa.
Hukumar FBI ta ce, kashe kansa ya yi kuma ta ce lamarin ba ya da wata alaka da mummunan laifi ko ta’addanci tunda Russell shi kadai ya shiga jirgin.