Dan takarar jam’iyyar NNPP, Barista M.B Shehu, ya lashe zaben kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Faggen Jihar Kano wanda aka gudanar a wannan Asabar din.
M.B Shehu ya doke dan Majalisar Tarayyar mai ci wanda yake wakiltar Karamar Hukumar Fagge, Aminu Sulaiman Goro na jam’iyyar APC.
- Alhassan Doguwa ya lashe zaben Majalisar Tarayya karo na biyar
- Ya gudu da budurwar mahaifinsa mako uku kafin daura musu aure
Goro wanda yake neman wa’adi na hudu ya sha kasa a hannun M.B Shehu wanda a yanzu shi zai ci gajiyar kujerar.
Da yake sanar da sakamakon, Baturen Zaben, Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya bayyana cewa, M.B Shehu ya samu kuri’u 19,024, yayin da dan takarar jam’iyyar LP, Shuaibu Abubakar ya samu kuriu 12,789.
Kamar yadda aka sanar da sakamakon zaben, Honarabul Goro ne ya zo na uku bayan samun kuri’u 8,669.
Tun da farko dai jam’iyyar NNPP ta bayar da ratar kuri’u 609 a yayin zaben da aka karasa, yayin da APC ta samu karin kuri’u 268 sai kuma jam’iyyar LP ta samu kuri’u 60.
Sai dai kuma bayan an lissafa da sauran kuriun da kowacce ta samu a yayin zaben na gama gari da aka gudanar a makonnin da suka gabata, jamiyyar NNPP ce ta zama zakara, yayin da LP ta zo ta biyu sai kuma APC ta biyo baya.
Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Asabar din ce ke karasa zabuka kusan 100 da suka rage, ciki har da na gwamnoni a jihohin Kebbi da Adamawa.
An bayyana zabukan a matsayin wadanda ba su kammala ba ne, lokacin babban zabe na kasa ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma na ranar 18 ga watan Maris.