A ranar Laraba, 8 ga watan Maris, 2023, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dage ranar zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha da aka shirya gudanarwa daga ranar 11 ga watan zuwa 18 ga wata.
Ga waiwayen lokutan da INEC ta dage babban zabe bayan dawowar Najeriya kan tafarkin dimokuradiyya shekara 24 da suka wuce (1999 zuwa 2023):
2011: Dage zabe bayan an fara kada kuri’a
A ranar 2 ga Afrilun 2011 INEC ta sanar da dage zaben Majalisar Dokoki ta Tarayya a yayin da ’yan Najeriya ke tsaka da jefa kuri’a a rumfar zabe.
Shugaban INEC na wannan lokacin, Farfesa Attahiru Jega, ya ce ya dage zaben ya zama dole saboda rashin isar kayan zabe a wasu sassan kasar da wuri.
Ya ce a lokacin da yake sanawar, duk da cewa an fara zabe a wasu jihohi, amma a wasu jihohin kayan zabe ba su je ba.
Ya ce, sannan “Takardun sakamakon zabe na da muhimmanci ga ingancin zabe, amma jami’anmu ba su isa rumfunan zabe da dama ba, kuma hakan zai kawo cikas ga tsarin zaben.”
Don haka ya dage zaben da kwana biyu zuwa ranar 4 ga watan Afrilu.
2015: An dage zabe da mako 6, sati guda kafin ranar zabe
INEC ta sanar cewa a shirye take ga gudanar da zaben shugaban kasa da majalisar dokoki ta kasa na 2015, amma mako guda kafin ranar zaben aka dage shi da mako shida, zuwa ranar 28 ga watan Maris.
Kasancewar matsalar Boko Haram na ganiyarta a yankin Arewa maso Gabas a lokacin, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro, Sambo Dasuki ya aika wa Jega wasika cewa, sojoji ba za su iya ba da tabbacin tsaro ba idan za a yi zaben yadda aka tsara da farko.
Don haka sojoji na bukatar karin lokaci su shirya, saboda haka zaben gwamonin da majalisar jiha ma aka dage shi zuwa ranar 11 ga watan Afrilu.
Jega ya ce INEC ta dage zaben ne domin babu yadda za a yi ta yi watsi da shawarar shugabannin tsaro ba.
2019: An dage zabe da tsakar dare
’Yan Najeriya sun wayi garin ranar zaben 2019 da jin cewa gab da asubahin ranar INEC ta dage shi, awa biyar kafin a fara jefa kuri’a.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, “Zaben ba zai yiwu ba, saboda ba a kammala jigilar kayan zabe ba, don haka dole a dage ranar don tabbatar da sahihin zabe.”
Saboda haka aka dage zaben shugaban kasa da majalisar dokoki ta kasa daga ranar 16 ga watan Fabrairu, zuwa ranar 23 ga wata.
Zaben gamnoni da majalisun dokokin jiha kuma aka mayar da shi 9 ga watan Maris,2019 maimakon ranar 2 ga wata.
2023: Saura kwana uku aka dage zaben gwamnoni
Kwana biyu kafin zaben gwamnoni a Majalisar Dokokin Jihohi na ranar 11 ga watan Maris, 2023, INEC ta dage shi da mako guda zuwa 18 ga wata.
Hukumar ta dage zaben ne sa’o’i kadan bayan ta samu izinin kotun domin loda sabbin bayanai a na’uarar BVAS ta tantance masu zabe, gabanin zaben jihohin.
Amma bayan wani zama da hukumar ta yi a ranar, ta sanar cewa zaben ba zai yiwu ba, saboda lokacin da ya rage ba zai isa ta kwashe bayanan zaben shugaban kasa da majalisar dokoki ta tarayya da ke cikin BVAS sama da 176,000 da aka yi amfani da su a zaben ranar 25 ga watan Maris ba.
Kakakin INEC, Barista Festus Okoye, ya bayyana cewa karar da wasu jam’iyyu suka shigar kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa suka samu izinin bincikar kayan zaben, ciki har da BVAS, ne ya kawo matsalar.
A cewarsa, ganin cewa kotun farko ba ta kayyade lokaci bincikar kayan zaben ba da kuma kurewar lokaci ne INEC ta je babbar kotu ta samu izinin sanya bayanan zaben gwamna da majalisar jiha a BVAS, saboda da su ne za a yi zaben.
Sai dai ya bayyana cewa ko lokacin da INEC ta samun izinin kotun, lokaci ya riga ya kure.