Liverpool ta sharara kwallo 7-0 a ragar Manchester United a Gasar Firimiyar Ingila ranar Lahadi a Anfield.
Liverpool ta ci kwallo biyu ta hannun Cody Gakpo, Darwin Nunez shi ma biyu ya zura a raga, Mohamed Salah ya ci biyu, sannan Roberto Firmino ya zura na bakwai.
Karon farko da Liverpool ta ci United kwallo da yawa a tarihin haduwar da suke yi, wasan farko da aka dura kwallo da yawa a ragar kungiyar Old Trafford tun bayan shekara 92.
Liverpool ta taba cin Manchester United 7-1 a Oktoban 1895 a gasar rukuni na biyu.
An kawo karshen wasa 12 da United ta buga a dukkan fafatawa ba tare da an doke ta ba, tun bayan 3-2 da Arsenal ta yi mata a Janairun 2023.
Kawo yanzu Mohamed Salah ya zama kan gaba a Liverpool a yawan cin kwallaye a Firimiyar Ingila a tarihi mai 129 a wasa 205.
Da wannan sakamakon Liverpool ta yi sama zuwa mataki na biyar da maki 42 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
Ita kuwa United wadda ta dauki Carabao Cup a bana tana ta ukun teburin da maki 49.
Liverpool za ta ziyarci Bournemouth ranar 11 ga watan Maris a Gasar Firimiyar Ingila, sannan kwana hudu tsakani ta fafata da Real a Santiago Bernabeu.
Real Madrid ta ci Liverpool 5-2 a wasan farko a zagayen ’yan 16 a Gasar Zakarun Turai ranar 21 ga watan Fabrairu.
Ranar 9 ga watan Maris, United za ta karbi bakuncin Real Betis a wasan farko a zagayen ’yan 16 a Europa League da za su fafata a Old Trafford.